Rikicin majalisar jihar Kaduna ya dau sabon salo: An dakatad da yan majalisa 3, an zajjara 5

Rikicin majalisar jihar Kaduna ya dau sabon salo: An dakatad da yan majalisa 3, an zajjara 5

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta dakatad da mambobinta uku daga shiga majalisar har na tsawon watanni tara kan laifin kawo hargitsi majalisar watanni biyu da suka gabata.

Hakazlaika majalisa ta zajjarar da mambobinta biyar kuma an umurcesu su aika wasikar neman afuwa tare da wallafawa a jarida na tsawon mako daya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto cewa yan majalisar sun yanke shawaran haka ne ranar Talata bayan kwamitin binciken hargitsin da ya faru ranar 11 ga Yuni ta kaddamar da sakamakon bincikenta a zauren majalisa.

Kwamitin karkashin jagorancin Shehu Yunusa, ta bada shawaran dakatad da su tare da zajjara wasu bisa dokokin majalisar.

Wadanda aka dakatar sune Mukhtar Isa-Hazo, tsohon mataimakin kakakin majalisar mai wakiltar mazabar Basawa; Nuhu Goroh-Shadalafiya, mai wakiltar mazabar Kagarko; da Yusuf Liman Dahiru, mai wakiltan Kakuri/Makera.

An dakatad da su bisa laifin raba kan yan majalisa tare da raina ofishin ga ofishin mataimakin kakaki.

Wadanda aka zajjara kuma sun hada da Salisu Isa (Magajin Gari), tsohon Kakaki Aminu Abdullahi-Shagali (Sabon Gari), AbdulWahab Idris (Ikara), Yusuf Salihu (Kawo) da Nasiru Usman (Tudun Wada).

Mataimakin Kakakin majalisar, Isaac Auta-Zankai ne ya jagoranci zaman.

KU KARANTA: Cacar baki ta kaure a kan hukuncin kashe matashi saboda batanci ga Annabi

Rikicin majalisar jihar Kaduna ya dau sabon salo: An dakatad da yan majalisa 3, an zajjara 5
Rikicin majalisar jihar Kaduna ya dau sabon salo: An dakatad da yan majalisa 3, an zajjara 5
Asali: UGC

A ranar 11 ga Yuni, 2020, an samu mummunan tashin hankali a majalisar jihar Kaduna a ranar Alhamis yayin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Makera, Dahiru Liman ya kwace sandar majalisar.

Mintuna kadan bayan sanar da tsige mataimakin kakakin majalisar, Dan majalisa Dahiru Liman ya shiga zauren majalisar tare da kwatar sandar majalisar don datse al'amarin da ke faruwa.

Amma kuma Dahiru Liman ya sha mugun duka a hannun 'yan majalisar da ke goyon bayan kakakin majalisa, Ibrahim Zailani yayin da ya yi yunkurin ficewa da sandar.

Wakilin Daily Trust da ya ga al'amarin lokacin da yake faruwa ya ce, da kyar sauran 'yan majalisa suka samu damar kwace shi daga hannun masu dukansa yayin da yake kokarin rike sandar.

Daga baya ne sauran 'yan majalisa suka yi kokarin fitar da shi bayan yayyaga kayansa da aka yi kuma jini yana zuba ta hancinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel