Cutar Coronavirus: Kawai mu koma ga Allah - Buhari ya yi wa'azi

Cutar Coronavirus: Kawai mu koma ga Allah - Buhari ya yi wa'azi

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa lamarin annobar Korona fa game duniya ce, kawai komawa ga Allah ne mafita daya tilo da ya rage mana.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin ganawarsa da kungiyar gwamnonin yankin Arewa maso yamma karkashin jagorancin gwamnan Borno, Babagana Zulum a fadarsa dake Aso Villa.

Ya daura laifin rashin samun nasarar yakin yan ta'addan Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya kan rashin isasshen kudi a baitul malin gwamnati da cutar COVID-19.

"Cutar COVID-19 wata irin abu ce ta daban. Ba ruwanta da launin fata, ba zaka iya shinshina ba, ba zaka iya ganinta ba, ba zaka jinta ba. Mun zama daya da Amurka, wannan wani abu ne mai ban mamaki. Ina ganin kawai mu koma ga Allah." Buhari ya fadi.

Cutar Coronavirus: Kawai mu koma ga Allah - Buhari ya yi wa'azi
Cutar Coronavirus: Kawai mu koma ga Allah - Buhari ya yi wa'azi
Asali: Twitter

A makon da ya gabata mun kawo muku rahoton cewa bankin Duniya ya amince da taimakawa Najeriya da kudi $114.28m domin kiyaye, gano da kawar da barazanar cutar Korona musamman a jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya.

Bisa jawabin da bankin ya saki ranar Juma'a, kudin taimakon ya hada da bashin $100 million daga kungiyar cigaban kasashen duniya IDA, sannan tallafin $14.28million daga asusun lamunin annoba na gaggawa.

Jawabin ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta bayar da tallafin ga jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya Abuja, ta kwamitin shiryawa da dakile cutar COVID-19 watau CoPREP.

Hakazalika yace shirin zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar Korona cikin unguwanni ta hanyar samar da dabaru na musamman.

A bangare guda, Bayan watanni takwas da bullarta a duniya, an samu rigakafin cutar Coronavirus na farko a duniya, Shugaban kasar jamhurriyar Rasha, Vladimir Putin, ya alanta.

Valdimir Putin ya ce ya amince da fara yiwa mutane alluran rigakafin saboda yana aiki sosai, kuma tuni an yiwa diyarsa.

A cewar jaridar Reuters, Rasha ce kasa ta farko a duniya da ta bada umurnin fara amfani da rigakafi a duniya, watanni biyu kacal bayan fara gwaji.

Yayinda yake magana a wata ganawa, Putin ya ce cibiyar Gamaleya ta kasar ce ta samar da rigakafin kuma yana bada kariya daga cutar Korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel