Yanzu-yanzu: Mun samu rigakafin Coronavirus ta farko a duniya, an yi 'diyata alluran - Shugaban kasan Rasha

Yanzu-yanzu: Mun samu rigakafin Coronavirus ta farko a duniya, an yi 'diyata alluran - Shugaban kasan Rasha

- An samu rigakafin cutar Korona ta farko a duniya

- Shugaban kasan Rasha ya ce an yiwa 'yar cikinsa

- Ya tabbatarwa duniya cewa rigakafin na samar da garkuwa mai karfi daga Coronavirus

Bayan watanni takwas da bullarta a duniya, an samu rigakafin cutar Coronavirus na farko a duniya, Shugaban kasar jamhurriyar Rasha, Vladimir Putin, ya alanta.

Valdimir Putin ya ce ya amince da fara yiwa mutane alluran rigakafin saboda yana aiki sosai, kuma tuni an yiwa diyarsa.

A cewar Reuters, Rasha ce kasa ta farko a duniya da ta bada umurnin fara amfani da rigakafi a duniya, watanni biyu kacal bayan fara gwaji.

Yayinda yake magana a wata ganawa, Putin ya ce cibiyar Gamaleya ta kasar ce ta samar da rigakafin kuma yana bada kariya daga cutar Korona.

"Na san rigakafin na aiki sosai, yana samar da garkuwan jiki mai karfi, kuma ina jaddada CEWA, rigakafin ya zarce duka matakan gwaji," Putin ya fadi.

Kawo ranar 31 ga Yuli, 2020, kungiyar lafiyar duniya WHO ta samu mutane 26 da ake yiwa gwajin rigakafin a mataki na karshe kuma ana gwajin mutane 139 a mataki na kusa da karshe.

Daga cikin wuraren da ake gwajin akwai jami'ar Oxford/AstraZeneca da kamfanin Pfizer..

KU KARANTA: Rashin kudi ke kawo mana tsaiko wajen yaki da yan Boko Haram - Buhari

Yanzu-yanzu: Mun samu rigakafin Coronavirus ta farko a duniya, an yi 'diyata alluran - Shugaban kasan Rasha
Shugaban kasan Rasha
Asali: UGC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel