Hotuna: Buhari yana ganawar sirri da gwamnoni da shugabannin tsaro
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a halin yanzu yana ganawa da wasu wakilan kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, da shugbannin hukumomin tsaro na kasar a fadarsa da ke Abuja.
Taron na da alaka da kokarin da gwamnatin ke yi na magance matsalar tabarbarewar tsaro a wasu sassan kasar kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Mai bawa Shugaban kasa shawara ta fanin tsaro, Babagana Monguna suma sun hallarci taron.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Yadda wani masanin magunguna ya mutu yayin gasar lalata da karuwa a otel
Kazalika, sauran shugabannin rundunar sojoji da hukumomin tsaro na kasar suma sun hallarci taron.
Wasu daga cikin gwamnonin da za su hallarci taron ta intanet sun hada da gwmanan Kogi, Yahaya Bello; Douye Diri na jihar Bayelsa; Babagana Zulum na jihar Borno; David Umahi na jihar Ebonyi da Babajide Sanwo Olu na jihar Legas.
A ranar Litinin, Buhari ya gana da gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas game dai da batun tsaron.
Ku saurari cikkaken rahoton ...
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng