Duniya juyi: Yadda tsohon dan majalisa ya koma kwasar bola (Hotuna)

Duniya juyi: Yadda tsohon dan majalisa ya koma kwasar bola (Hotuna)

- Oluomo Segun Olulade wanda aka fi sani da Eleniyan, tsohon dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Epe ta II, wanda ke da kamfanin kwasar shara

- A wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram, tsohon dan majalisar ya bayyana yaddda ya gyara kamfaninsa da amfanin mayar da hankali

- Segun ya yi dan majalisar jihar a Legas har sau biyu amma yanzu yana da kamfanin kwasar bola

Tsohon dan majalisa, Oluomo Segun Olulade, wanda ya wakilci mazabar Epe ta II, ya koma kasuwancin kwashe shara.

Kamar yadda ya sanar, an haifesa a ranar 20 ga watan Yulin 1971 kuma ya fara karatunsa a Epe kafin ya karasa jami'ar jihar Legas inda ya yi digirinsa a kan tsumi da tattali.

Kasuwancinsa a yanzu na kwasar bola, ya fara ne daga yadda yake son gyaran muhalli da kuma shawo kan matsalolinsa.

Duniya juyi: Yadda tsohon dan majalisa ya koma kwasar bola (Hotuna)
Duniya juyi: Yadda tsohon dan majalisa ya koma kwasar bola (Hotuna). Hoto daga Oloumo
Asali: UGC

Bayan manyan nasarorin da ya samu a fannin tsaftace muhalli, ya fada harkar siyasa inda ya yi wakilci a majalisar jihar har sau biyu.

Kamar yadda ya nuna, shine dan majalisa na farko da ya fara koyarwa ta rediyo tun daga tushe.

A ranar Litinin, 10 ga watan Augusta, ya wallafa hotuna da bayani a kan kamfaninsa na kwasar shara inda yayi magana a kan jajircewa.

Hotunan da ya wallafa a shafinsa na Instagram ya bayyana tare da daya daga cikin manyan motocin kamfaninsa na dibar shara.

Duniya juyi: Yadda tsohon dan majalisa ya koma kwasar bola (Hotuna)
Duniya juyi: Yadda tsohon dan majalisa ya koma kwasar bola (Hotuna). Hoto daga Oloumo
Asali: UGC

KU KARANTA: Ka yi amfani da kujerarka wurin kawo hadin kai a arewa - Matawalle ga Sarkin Kano

A wani labari na daban, kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tura 'yan sanda don yakar Boko Haram a yankin, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a wata takarda da ta fitar bayan taronta karo na biyu da tayi don tattaunawa a kan kalubalen da yankin ke fuskanta.

Takardar ta samu saka hannun shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.

Ta jinjinawa kokarin gwamnatin tarayya wurin yaki da ta'addancin, amma tayi kira ga dakarun soji da su tsananta tsaro wurin tabbatar da cewa manoma a yankin za su iya komawa gonakinsu.

"Kungiyar ta bukaci cewa , a rufe gibin rashin ma'aikata isassu ta hanyar tura jami'an 'yan sanda don tsaro sannan a samar musu da kayayyakin aiki isassu," takardar tace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel