Rashin kudi ke kawo mana tsaiko wajen yaki da yan Boko Haram - Buhari

Rashin kudi ke kawo mana tsaiko wajen yaki da yan Boko Haram - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya daura laifin rashin samun nasarar yakin yan ta'addan Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya kan rashin isasshen kudi a baitul malin gwamnati.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin ganawarsu da kungiyar gwamnonin yankin Arewa maso yamma a fadarsa dake Aso Villa.

Ya kara da cewa cutar Korona ce ta kara tsananta lamarin.

Amma ya ce akwai damuwa matuka bisa yadda matsalar tsaro ke tsananta fiye da yadda ya samu abin lokacin da ya dau ragamar mulki.

"Muna da matsalan rashin kudi da rashin tsaro. Kun san gado mukayi. Amma ya kamata Al'ummar Arewa maso yamma su godewa abinda gwamnatin nan tayi." Buhari yace

"Rahoton da nike samu, da kuma labaran leken asiri shine hukumar Soji ta sake zanga dantse kuma wannan shine gaskiyan lamari."

"Na kan samu labaran akai-akai kuma ya zama wajibi in yarda yanzu. Na saurari jawabanku, gwamnan dake samun matsala yanzu a Arewa maso gabas, Adamawa, Bauchi da sauransu na jin dadin zaman lafiya yanzu. Ina kyautata zaton suna godiya bisa sadaukarwan da Soji sukayi."

"Ina tabbatar muku da cewa gwamnati na iyakan kokarinta. Rashin kudi ya zame mana kalubale."

Rashin kudi ke kawo mana tsaiko wajen yaki da yan Boko Haram - Buhari
Rashin kudi ke kawo mana tsaiko wajen yaki da yan Boko Haram - Buhari
Asali: Facebook

KU KARANTA: Bankin duniya ya amince da baiwa Najeriya $114.28m don yakar cutar Korona

A bangare guda, Babban Hafsan Sojin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa jami'ansa sun fitittiki yan ta'addan Boko Haram daga dukkan jihohin Arewa maso gabashin Najeriya face jihar Borno.

Buratai ya bayyana hakan ne yayinda ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari ranar Litinin, 10 ga Agusta, 2020, Premium Times ta gani.

Hafsan Sojan, ya kara da cewa yanzu haka jami'ansa na amfani da labaran leken asiri domin kawar da yan ta'addan daga Borno.

"Babu yan Boko Haram a sauran jihohin dake makwabtaka. An fitittikesu, yanzu suna boye a jihar Borno,"

"Muna aiki tare da masu fararen hula da sarakunan gargajiya, abinda muke bukata kawai shine hakuri. Ba zamuyi kasa a gwiwa ba." ya bayyana a jawabin da kakakin Buhari, Garba Shehu ya fada.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel