An ceto yaron da aka tilastawa rayuwa tare da dabobi na shekaru 2 a Kebbi

An ceto yaron da aka tilastawa rayuwa tare da dabobi na shekaru 2 a Kebbi

A safiyar ranar Lahadi 9 ga watan Agustan 2020, wata tawaga daga gwamnatin Jihar Kebbi ta karbi Jamilu Aliyu, yaro mai shekara 10 da iyayensa suka tilasta masa rayuwa tare da dabobi na tsawon shekaru biyu.

An saka wa Aliyu mari ne aka kuma jefa shi cikin akuyoyi da sauran dabobi yana rayuwa cikin su na tsawon shekaru biyu bayan mahaifiyarsa ta rasu.

Lamarin ya faru ne a garin Badariya na jihar Kebbi da ke karamar hukumar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya kamar yadda HumAngle ta ruwaito.

Yaron na zaune ne tare da mahaifinsa da kishiyoyin mahaifiyarsa biyu inda ake hana shi abinci wasu lokutan na makonni ko watanni hakan ya sa ya ke cin abincin da ake bawa dabobin ko kuma ya ci bayan gidan dabobin.

An ceto yaron da aka tilastawa rayuwa a keji tare da dabobi na shekaru 2 a Kebbi
An ceto yaron da aka tilastawa rayuwa a keji tare da dabobi na shekaru 2 a Kebbi. Hoto daga HumAngle
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda wani masanin magunguna ya mutu yayin gasar lalata da karuwa a otel

Makwabta ne suka gano yaron kuma cikin kankancin lokaci labarin ya bazu tare da faifan bidiyo da aka nada.

Da taimakon Kungiyar Lauyoyi Mata da Hukumar Kiyayye Hakkin Yan Adam, gwamnati ta kawo masa dauki inda aka same shi ya rame sosai kuma wasu halayensa sun sauya sun koma irin na dabobi.

Yan sanda sun kama mahaifin yaron, Aliyu Badariya da matansa biyu inda ak tsare su a Kebbi yayin da aka tafi da yaron asibiti domin ya samu kulawan likitoci.

Hajiya Zarau Wali, mashawarciyar gwamnan Kebbi kan Harkokin Mata da Cigaba ta ziyarci yaron a asibitin tunawa da Sir Yahaya da ke Birnin Kebbi inda ta ce, "Za a duba shi kuma gwamnati za ta dauki nauyin dawainiyar masa magani."

Wani lauya mai kare hakkin bil adama, Hamza Attahiru Wala ya ce, "An samu Jibrilu daure tare da dabobi inda ya ke cin bayan gidan dabobin, iyayen sa sun ce wai Jibirilu yana fama da ciwon farfadiya ne."

Shugaban karamar hukumar Birnin Kebbi, Alh Aminu Ahmad Sarkin Fada, ya bayyana kaduwarsa game da lamarin inda ya yi alkawarin cewa jihar za tayi duk mai yiwuwa don yiwa yaron magani tare da hukunta iyayen.

Ya yi kira ga mutanen gari musamman shugabannin al'umma su rika saka idanu kuma su kai rahoton duk wani da aka gano yana cin zarafin yara.

A bangarensa, gwamnan jihar Mr Abubakar Bagudu shime ya nuna bakin cikinsa game da afkuwar lamarin.

Tun a baya gwamnan ya mika wa majalisar jihar kudirin dokar kiyayye hakkin yara amma har yanzu ba a amince da kudin ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel