Covid-19: Kananan hukumomi 85 na jihohi 20 a tarayya suna nan ba tare da an yi gwaji ba - Boss Mustapha

Covid-19: Kananan hukumomi 85 na jihohi 20 a tarayya suna nan ba tare da an yi gwaji ba - Boss Mustapha

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa akwai kananan hukumomi 85 na wasu jihohi 20 da har yanzu suna nan ba tare da gwajin gano masu dauke da kwayoyin cutar korona a cikinsu ba.

Haka kuma Gwamnatin ta bayyana cewa, har kawo yanzu babu wani rahoto da aka samu daga kananan hukumomin cewa an gano wanda cutar korona ta harba a cikinsu duk da annobar tana ci gaba da yaduwa babu sassauci.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya sanar da hakan yayin zaman karin haske karo na 56 da aka gudanar kan matakin annobar korona a kasar.

A cewar Mista Mustapha wanda shi ne shugaban kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona PTF, ya ce akwai bukatar a bunkasa harkokin gwaje-gwajen gano masu dauke da cutar a kasar nan.

Kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona a Najeriya, PTF
Kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona a Najeriya, PTF
Asali: Twitter

Cikin jawabinsa, “binciken mu ya gano cewa jihohi biyar sune suka tattara kasha 60 cikin dari na mutanen da cutar korona ta harba a kasar.”

“Daga cikin kananan hukumomi 774 da Najeriya ta kunsa, 689 sun samu bullar cutar a cikinsu.”

“Kananan hukumomi 85 a jihohi 20 har yanzu suna nan ba tare da an yi gwajin gano masu cutar a cikinsu ba, kuma babu wani rahoto da aka samu na bullar cutar a cikinsu.”

“Haka kuma kaso 50 cikin 100 na duk masu dauke da kwayoyin cutar a fadin kasar sun tattara ne a kananan hukumomi 20,” inji Sakataren Gwamnatin.

KARANTA KUMA: Cutar korona ta hallaka mutum 950 a Najeriya - NCDC

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kwamitin da sakataren Gwamnatin ke jagoranta ya zargi gwamnonin jihohi, sarakunan gargajiya da malaman addini da jawo cincirindo.

PTF ta ce laifin manyan kasar ne ya jawo mutane su ka rika yin cinkoso wajen gangamin yakin neman zaben gwamna a jihar Edo, da kuma jana’izar Buruji Kashamu a Ogun.

A ranar 10 ga watan Agusta, kwamitin PTF ya zanta da manema labarai kamar yadda ya saba lokaci bayan lokaci, kwamitin ya yi takaicin abubuwan da su ka faru kwanan nan.

Sanata Buruji Kashamu ya mutu ne bayan ya yi fama da COVID-19. An binne shi a Ijebu, Ogun, inda mutane rututu su ka sabawa sharudan da PTF ta gindaya na dakile yaduwar korona.

Hakan nan jam’iyyun APC da PDP sun shirya gangamin yakin neman zaben gwamnan Edo. A nan ma dinbin mutane sun samu halarta inda galibinsu basu rufe fuskokinsu da takunkumi ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel