Gwamna ya kori hadiminsa sa'o'i kadan bayan shagalin bikin diyarsa

Gwamna ya kori hadiminsa sa'o'i kadan bayan shagalin bikin diyarsa

- Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya kori babban sakataren yada labaransa bayan sa'o'i kadan da yin bikin diiyarsa

- Kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana, hakan ba zai rasa alaka ba da bacin lokacin da aka samu wurin daurin auren

- Amma kuma mataimakinsa na musamman wurin yada labarai ya ce ba haka bane, korar ta zo ne daga ofishin shugaban ma'aikata

Gwamnan Ishaku Darius na jihar Taraba ya sallami Alhaji Hassan Mijinyawa, babban sakataren yada labaransa.

Ya sallamesa ne a ranar Asabar inda ya maye gurbinsa da mataimakinsa, Iliya Becky.

Ana rade-radin cewa sallamar na da alaka da yadda aka bata lokaci a yayin daurin auren diyarsa a Jalingo.

Jiga-jigan da suka samu halartar wurin daurin auren sun hada da mataimakin gwamnan, Alhaji Hassan Manu, wanda ya isa gidan korarren CPS din ana sauran mintoci biyu kafin karfe 10 na safe wanda shine lokacin daurin auren.

Amma kuma a maimakon a fara daurin aure, jaridar The Nation ta gano cewa an tsaya jiran ministan wutar lantarki, Alhaji Saleh Maman, wanda ke kan hanyar zuwa.

Hakan ya sa an kwashe tsawon mintoci ana wannan jiran kafin daga bisani su iso wurin daurin auren.

Gwamna ya kori hadiminsa sa'o'i kadan bayan shagalin bikin diyarsa
Gwamna ya kori hadiminsa sa'o'i kadan bayan shagalin bikin diyarsa. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mai Deribe: Mamallakin fadar zinari a Najeriya da ke saukar manyan shugabannin duniya

An gano cewa mataimakin gwamnan da sauran jiga-jigan sun yi tsayuwar kusan minti 30 kafin isowar ministan da tawagarsa.

Sauran majiyoyin sun ce mataimakin gwamnan tare da tawagarsa sun bar wurin walima a fusace kuma da gaggawa.

Bayan barinsu wurin da sa'o'i biyu, an sanar da sallamar Mijinyawa daga aiki, wanda wasu ke zargin cewa bacin lokaci wurin daurin auren ne ya janyo hakan.

Amma kuma babban mai bai wa gwamna Ishaku shawara a fannin yada labarai, Bala Abu, ya musanta sallamar da wannan alakar.

"Kamar yadda aka sani, jawabin 'yan jarida na tube CSP daga kujerarsa ya fito ne daga ofishin shugaban ma'aikatan jihar. Wannan na nuna cewa babu alaka tsakanin hakan da wani abu na daban. Cikin aiki ne," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel