Mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta 46,000 - NCDC
Babu shakka hukumomin lafiya na ci gaba da aiki tukuru domin dakile yaduwar cutar korona a Najeriya, sai dai fa lamarin ya ci tura domin kuwa cutar na ci gaba da bazuwa babu sassauci.
A halin yanzu an samu bullar cutar covid-19 a duk jihohi 36 na Najeriya da kuma babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbatar.
Taskar bayanai ta NCDC a ranar Lahadi, 9 ga watan Agustan 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 46,577 yayin da mutum 33,186 suka samu waraka.
Ya zuwa yanzu dai mutane 945 cutar ta hallaka a fadin Najeriya kamar yadda hukumar NCDC ta fidda bayanan alkalumanta.

Asali: Facebook
Rumbun tattaro bayanai na NCDC ya nuna cewa, an yi wa mutum 317,496 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020.
Haka kuma alkaluman cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 12,446 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.
KARANTA KUMA: Hadin gwiwar dakarun soji: Kwararre ya yi hasashen ta'addanci zai zamo tarihi a Najeriya ba jimawa
Da misalin karfe 11.17 na jiya Lahadi da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 437 da cutar ta harba a fadin Najeriya.
Sabbin mutane 437 da cutar ta harba cikin jihohi 17 sun kasance kamar haka:
Legas (107), Abuja (91), Filato (81), Kaduna (32), Ogun (30), Kwara (24), Ebonyi (19), Ekiti (17), Oyo (8), Borno (6), Edo (6), Kano (4), Nasarawa (3), Osun (3), Taraba (3), Gombe (2) da Bauchi (1).
Har kawo yanzu jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, sai kuma birnin Abuja a mataki na biyu yayin da jihar Oyo ta biyo bayansu a mataki na uku.
Ga jerin adadin mutanen da cutar ta harba cikin kowace daya daga cikin jihohi 36 na Najeriya da cutar ta bulla:
Lagos - 15,875
Abuja - 4,467
Oyo - 2,868
Edo - 2,382
Ribas - 1,939
Kano - 1,626
Kaduna - 1,598
Delta - 1,596
Plateau - 1,502
Ogun - 1,469
Ondo - 1,284
Enugu - 905
Ebonyi - 870
Kwara - 857
Katsina - 746
Borno - 688
Abia - 644
Gombe - 631
Osun -628
Bauchi - 577
Imo - 476
Benue - 409
Nasarawa - 370
Bayelsa - 346
Jigawa - 322
Akwa Ibom - 235
Niger -226
Adamawa - 185
Ekiti - 178
Sokoto -154
Anambra -142
Kebbi - 90
Zamfara - 77
Taraba - 75
Kuros Riba - 68
Yobe - 67
Kogi - 5
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng