Yajin Aiki: ASUU za ta koma teburin sulhu da Gwamnatin Tarayya

Yajin Aiki: ASUU za ta koma teburin sulhu da Gwamnatin Tarayya

Alamu masu karfi sun bayyana a karshe mako cewa gwamnatin tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i, za su koma kan teburin sulhu domin kawo karshen yajin aikin malamai suka shafe watanni hudu suna yi.

Binciken manema labarai na jaridar This Day ya gano cewa, nan ba da dadewa ba, bangarorin biyu za su fara tattaunawa domin sulhunta sabanin da ke tsakaninsu.

Bangarorin biyu za su koma kan teburin sulhu domin sabunta tattaunawa kan rashin jituwar da ke tsakaninsu musamman a kan sabon tsarin biyan albashi na bai daya da gwamnatin ta dage a kan sanya malaman jami’o’i cikinsa.

Shugaban ASUU; Farfesa Biodun Ogunyemi
Hoto daga kamfanin dillancin labarai na kasa
Shugaban ASUU; Farfesa Biodun Ogunyemi Hoto daga kamfanin dillancin labarai na kasa
Asali: UGC

Watsi da wannan sabon tsari ya sanya gwamnati ta yanke shawarar dakatar da biyan albashin dukkan malamai mambobin ASUU da suka ki shiga tsarin.

Ita kuwa kungiyar ASUU ta tsaya kacokan a kan kawo tsarin biyan albashin ma’aikatan jami’o’i na daban da wanda gwamnatin tarayya ta assassa, lamarin da ya kawo rabuwar kai a tsakaninsu.

Yayin zantawa da manema labarai a karshen mako, shugaban ASUU Farfesa Biodun Ogunyemi, ya ce kungiyar ta gana da Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu, domin ya agaza a kan komawa teburin sulhu da gwamnatin tarayya.

KARANTA KUMA: Sanatoci 3 sun kaurace wa taron jam'iyyar PDP a Ebonyi

Haka kuma Ministan Kwadago Dakta Chris Ngige, ya tabbatar da cewa kiris ya rage ya gayyaci kungiyar ASUU domin a koma kan teburin sulhu inda za a ci gaba da tattauna don cimma matsaya.

Farfesa Ogunyemi ya ce ASUU a shirye take ta koma kan teburun sulhu, amma dai babu wani goron gayyata da ta samu tukunna.

Da yake amsa tambaya kan ko kungiyar za ta janye yajin aikin don ba da damar jami’o’in su sake budewa, Ogunyemi ya ce: “Mun yi imani idan gwamnatin tarayya ta kasance da gaskiya, mambobinmu za su koma aiki da zaran mun warware sabanin da ke tsakaninmu.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel