Sanatoci 3 sun kaurace wa taron jam'iyyar PDP a Ebonyi
Sanatoci uku da suka fito daga jihar Ebonyi da kuma wani dan majalisar wakilai ta tarayya, na daga cikin sanannun kusoshin jam’iyya da suka kauracewa taron PDP a jihar.
‘Yan majalisar dattawan da bas u halarci taron ba sun hadar da; Sanata Egwu mai wakiltar Ebonyi ta Arewa; Sanata Ama Nnachi mai wakiltar Ebonyi ta Kudu, da kuma Sanata Obinna Ogba mai wakiltar Ebonyi ta Tsakiya.
Daga bangaren majalisar wakilai kuma, Honarabul Iduma Igariwey, mai wakiltar mazabar Afikpo ta Arewa ta Kudu, shi ma bai halarci taron jam’iyyar ba.

Asali: UGC
Hakan na zuwa ne yayin da a taron aka zabi sabbin shugabanni da za su jagoranci harkokin gudanarwa na jam’iyyar cikin shekaru hudu masu zuwa.
Babu dalilai da aka bayyana dangane da rashin halarcinsu a taron, sai dai ana iya danganta shi da zargin da ake musu na nuna bukatar sabbin shugabannin jam’iyya na jihar gabanin babban zaben kasa na 2023.
A dalilin haka ne Gwamna David Umahi yayin taron, ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da a zauna lafiya cikin aminci, lamarin da ya ce babu dalilin kawo rikici a tsakanin al’umma.
KARANTA KUMA: A cikin sabon bidiyo, Shekau ya yi wa Shettima, Zulum, Monguno, Bukarti da Dalung barazana
Dangane da fusatattun ‘yan majalisar tarayya da suka kauracewa taron, Gwamna Umahi ya yi rarrashi tare da neman shugabannin jam’iyyar su yi wani zama na musamman a ranar Alhamis domin neman sulhu.
A cewarsa, “ni ne uban gayya na jam’iyyar PDP a jihar kuma mun yi aiki tare a shekarar 2015 da kuma 2019.”
“Saboda haka babu wani dalili da zai kawo rabuwar kai a yanzu, duk abinda ya shige mana duhu, to mu hadu a ranar Alhamis domin sulhunta duk wani sabani. Wannan yana da matukar muhimmanci.”
A wani rahoton Legit.ng ta ruwaito cewa, ‘Dan takarar mataimakin gwamnan jihar Edo a karkashin jam’iyyar APC, Gani Audu, ya shiga cikin tsaka mai wuya a dalilin zargin rashin gaskiya a kan wasu takardunsa.
A ranar Lahadi, 9 ga watan Agusta, Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta karbi wasu takardu da ke zargin Mista Gani Audu da yin karya a game da satifiket dinsa.
Takardun da aka mikawa hukumar zabe na kasa ta INEC sun nuna tun farko akwai kwan-gaba-kwan-baya game da sunan ‘dan takarar da kuma takardun shaidar da ya bada.
An samu wannan matsala ne a wasu takardun Gani Audu wanda hakan na iya jawowa jam’iyyar APC mai hamayya ta rasa kujerar gwamnan jihar Edo, ko da ta yi nasara a zaben.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng