Yan Najeriya na sauraron yadda karshenka zata kasance - Fayose ya caccaki Obasanjo kan isgilinsa ga marigayi Kashamu

Yan Najeriya na sauraron yadda karshenka zata kasance - Fayose ya caccaki Obasanjo kan isgilinsa ga marigayi Kashamu

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya caccaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kalaman isgilin da ya yiwa marigayi Sanata Buruji Kashamu.

Olusegun Obasanjo, ya aika sakon ta'azziyarsa ga gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, bisa rasuwar Sanata Buruji Kashamu.

A wasikar da ya aike ranar Asabar, 8 ga Agusta, Obasanjo ya siffanta mutuwar Kashamu a matsayin babban abin rashi.

Yace: "Rayuwa da tarihin mamacin ya barmu da darrusa da dama."

"Sanata Esho Jinadu (Buruji Kashamu) a rayuwarsa yayi amfani da lauyoyi da siyasa wajen sullubewa doka kan laifukan da aka zargin ya aikata a Najeriya da wajen Najeriya. Amma babu wani wayon lauyoyi, siyasa, al'ada ko ma na likitoci da ya hana mutuwar riskarsa lokacin da mahallici yace lokaci ya yi."

Amma martani kan jawabin Obasanjo, Fayose, yace maganar Obasanjo abin kunya ne.

"Abin takaici ne abinda Obasanjo yake fadi kan Buruji Kashamu bayan mutuwarsa don ya san ba zai iya ramawa ba. Me yasa bai fadi hakan lokacin da Kashamu ke raye ba?" Fayose ya ce.

Fayose ya cigaba da tambayan Obasanjo cewa "shin zai iya fadi cewa bai taba hada hannu da Kashamu a lokacin da suka siyasarsu bane?"

"Yan Najeriya na sauraran yadda karshen Obasanjo zata kasance. Ya daina kokarin nunawa mutane shi wani Waliyyi ne saboda mun san ba waliyyi bane. Ya tuna cewa karshensa zata zo kuma babu wanda ya san yadda karshen zata kasance."

KU KARANTA: Matashin ya sha kusa hallaka kansa don Maryam Yahaya ya sake komawa Kano, sai ya ganta

Yan Najeriya na sauraron yadda karshenka zata kasance - Fayose ya caccaki Obasanjo kan isgilinsa ga marigayi Kashamu
Yan Najeriya na sauraron yadda karshenka zata kasance - Fayose ya caccaki Obasanjo kan isgilinsa ga marigayi Kashamu
Asali: UGC

Sanatan wanda ya wakilci mazabar jihar Ogun ta gabas kuma tsohon dan takaran kuneran gwamnan jihar, Buruji Kashamu, daga shekarar 2015 zuwa 2019 ya mutu ne bayan kamuwa da cutar Coronavirus.

Ya rasu ne ranar Asabar, 8 ga Agusta a wani Asibitin jihar Legas yana mai shekaru 62.ThisDay ta ruwaito.

Daya daga cikin abokan aikinsaa tsohuwar majalisa, Sanata Ben Murray Bruce, ne ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel