Kashamu: Wayon siyasarsa bai hana mutuwa riskarshi ba - Obasanjo ya aika sako ta'aziyya ga iyalan Sanatan

Kashamu: Wayon siyasarsa bai hana mutuwa riskarshi ba - Obasanjo ya aika sako ta'aziyya ga iyalan Sanatan

-Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya aika sakon ta'azziyar mutuwarSanata Buruji kashamu ga gwamna Abiodun

-Obasanjo ya ce yayinda Kashamu ke da rai, ya yi amfani da siyasa da lauyoyi wajen sullubewa doka bisa manan laifukan da ake zarginshi da su gida da waje

- Amma tsohon shugaban kasa ya yi addu'an Allah ya jikansa kuma bashi Aljannah

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya aika sakon ta'azziyarsa ga gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, bisa rasuwar Sanata Buruji Kashamu.

A wasikar da ya aike ranar Asabar, 8 ga Agusta, Obasanjo ya siffanta mutuwar Kashamu a matsayin babban abin rashi.

Wasikar yace: "Na samu labari mara dadi na mutuwa rSanata Esho Jinadu (Buruji Kashamu), dan jihar Ogun mai muhimmanci. Ina mika sakon ta'aziyyata da na iyali na bisa wannan rashi.

"Rayuwa da tarihin mamacin ya barmu da darrusa da dama."

"Sanata Esho Jinadu (Buruji Kashamu) a rayuwarsa yayi amfani da lauyoyi da siyasa wajen sullubewa doka kan laifukan da aka zargin ya aikata a Najeriya da wajen Najeriya. Amma babu wani wayon lauyoyi, siyasa, al'ada ko ma na likitoci da ya hana mutuwar riskarsa lokacin da mahallici yace lokaci ya yi."

"Allah ya gafarta masa zunubansakuma ya sa shi a Aljannah."

Kashamu: Wayon siyasarsa bai hana mutuwa riskarshi ba - Obasanjo ya aika sako ta'aziyya ga iyalan Sanatan
Kashamu: Wayon siyasarsa bai hana mutuwa riskarshi ba - Obasanjo ya aika sako ta'aziyya ga iyalan Sanatan
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta kashe Bilyan 14 kan ciyar da dalibai, N-Power da CCT a jihar Jigawa kadai

Rahotanni sun bayyana cewa Kashamu ya mutu ne bayan kamuwa da cutar Coronavirus.

Ya rasu ne ranar Asabar, 8 ga Agusta a wani Asibitin jihar Legas yana mai shekaru 62.ThisDay ta ruwaito.

Daya daga cikin abokan aikinsaa tsohuwar majalisa, Sanata Ben Murray Bruce, ne ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita.

Yace: "Yanzu na rasa babban abokina har abada sakamakon COVID19. Har ya rasu, Sanata Kashamu da ne mun kasance tare."

"Ya rasu ne a asibitin First Cardiology Consultants dake Lagos."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel