COVID-19: Yan Nigeria 311 sun dawo daga UAE, sun sauka Abuja

COVID-19: Yan Nigeria 311 sun dawo daga UAE, sun sauka Abuja

A yayin da annobar COVID-19 ke ci gaba da yin barna a kasashen duniya, 'yan Nigeria dari hudu da goma sha daya ne suka iso babban birnin tarayya Abuja, daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Hukumar 'yan Nigeria mazauna kasashen waje (NIDCOM) ta bayyana hakan a ranar Asabar, a shafinta na Twitter.

Da wannan ne adadin 'yan Nigeria da aka kwaso daga UAE ya zama 2,353 yayin da ake sa ran kwaso sauran 'yan Nigeria da suka makale a daular.

"Jirgin Fly Emirates mai dauke da fasinjoji 311 ya iso tashar jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe, Abuja da misalin karfe 11:50 na ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, 2020, daga UAE," a cewar NIDCOM.

Wadanda aka maido din, ana sa ran zasu kasance a killace domin cika sharuddan da kwamitin fadar shugaban kasa da hukumar NCDC, na dakile yaduwar cutar COVID-19.

KARANTA WANNAN: Buhari da Atiku sun aika sakon ta'aziya ga iyalan Isyaku Rabiu da Sanata Kashamu

COVID-19: Yan Nigeria 311 sun dawo daga UAE, sun sauka Abuja
COVID-19: Yan Nigeria 311 sun dawo daga UAE, sun sauka Abuja
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne awanni 24 bayan da aka maido wasu 'yan Nigeria 331 daga Hadaddiyar Daular Larabawan.

Wadanda aka maido din, anyi masu gwaji kuma an gano basa dauke da cutar COVID-19, sai dai duk da hakan za a killace su na tsawon kwanaki 14 don tabbatar da gwajin.

Tun bayan da annobar COVID-19 ta barke a duniya, dubunnan 'yan Nigeria da ke zaune a wasu kasashen ne aka samu nasarar kwaso su tare da maido su gida.

A farkon watan Yuni, gwamnatin tarayya ta ce ta kashe N169m a jigilar 'yan Nigeria daga kasashen da suke zuwa gida Nigeria.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel