Yanzu-Yanzu: Sanata Buruji Kashamu ya mutu

Yanzu-Yanzu: Sanata Buruji Kashamu ya mutu

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa tsohon Sanata mai wakiltan mazabar jihar Ogun ta gabas kuma tsohon dan takaran kuneran gwamnan jihar, Buruji Kashamu, ya mutu.

Rahotanni sun bayyana cewa Kashamu ya mutu ne bayan kamuwa da cutar Coronavirus.

Ya rasu ne ranar Asabar, 8 ga Agusta a wani Asibitin jihar Legas yana mai shekaru 62.ThisDay ta ruwaito.

Daya daga cikin abokan aikinsaa tsohuwar majalisa, Sanata Ben Murray Bruce, ne ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita.

Yace: "Yanzu na rasa babban abokina har abada sakamakon COVID19. Har ya rasu, Sanata Kashamu da ne mun kasance tare."

"Ya rasu ne a asibitin First Cardiology Consultants dake Lagos."

Yanzu-Yanzu: Sanata Buruji Kashamu ya mutu
Yanzu-Yanzu: Sanata Buruji Kashamu ya mutu
Asali: Depositphotos

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel