Bauchi: Dubban yan PDP sun dunguma sun koma APC a mazabar Dogara

Bauchi: Dubban yan PDP sun dunguma sun koma APC a mazabar Dogara

Kimanin makonni biyu bayan komawar tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara zuwa jamiyyar APC, magoya bayansa a karamar hukumar Bogoro da ke cikin mazabansa suma sun fice daga PDP.

Idan za a iya tunawa, Dogara mai wakiltar mazabun Dass/Tafawa Balewa/Bogoro a majalisar wakilai na tarayya ya fice daga PDP ne sakamakon rashin jituwa da ta shiga tsakaninsa da gwamnan jihar, Sen. Bala Mohammed.

A yayin karbar sabbin yan jamiyyar a karamar hukumar Bogoro, Shugaban jamiyyar APC, Haruna Rikayar a ranar Asabar ya tabbatar musu da cewa ba za a nuna musu banbancin ba kuma ya bugi kirjinsa ya ce jamiyyar APC ta fara kwace jihar.

Yan PDP fiye da 1,000 sun koma APC a mazabar Dogara
Yan PDP fiye da 1,000 sun koma APC a mazabar Dogara
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yan sanda sun kama Manjo ɗin Soja na bogi ɗauke da wiwi masu yawa (Hotuna)

Wadanda suka sauya jamiyyar sun ce sun dawo APC ne tunda dama nan ne gidansu na ainihi. Bulus Iliya, daya daga cikin magoya bayan Dogara, kuma mai neman takarar shugaban karamar hukumar Bogoro ne ya musu jagoranci.

Iliya, ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne domin su cigaba da tafiya tare da mai gidansa na siyasa inda ya jadadda cewa zai cigaba da yi masa biyayya.

Ya kuma yi kira ga gwamnan jihar Bala Mohammed ya yi gaskiya da adalci yayin gudanar da zabukan kananan hukumomi da za ayi a jihar.

Bulus ya ce ya yi nadamar komawa PDP domin su magoya bayan Dogara an mayar da su ware ne a can jamiyyar ta PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel