Hudu sun mutu, 3 sun makance bayan shan sunadarin tsaftace hannu 'Hand Sanitizer'

Hudu sun mutu, 3 sun makance bayan shan sunadarin tsaftace hannu 'Hand Sanitizer'

Akalla mutane hudu aka ruwaito sun rasa rayukansu a kasar Amurka bayan shan sunadarin tsaftace hannu daga cuta da turawa ke kira da 'Hand Sanitizer'.

Haka cibiyar hana aukuwa da yaduwar cututtuka a Amurka CDC ta sanar inda tace ta samu kiraye-kiraye 15 da na masu fama da azabar gubar Methanol sakamakon shan sundarin tsaftace hannu a watannin baya.

A cikin mutanen nan 15, hudu sun mutu a jihar Arizona da New Mexico tsakanin watan Mayu da Yuni, a cewar rahoton da hukumar CDC Amurka ta wallafa ranar Laraba kumaThe Nation ta gani.

Daga cikin mutane hudu da suka mutu, uku sun kamu da buguwar kwakwalwa tamkar farfadiya kuma aka kwantar da su a Asibiti.

Wasu uku kuma sun rasa ganinsu bayan sallamarsu daga Asibiti.

A watan Yuli, hukumar kula da sihhancin Magunguna da Abinci ta yi gargadin cewa "Methanol wani sunadari ne dake da illa ga jikin mutum kuma ya kan yi kisa idan aka hadiya."

Hukumar CDC na Amurka ta ce wanke hannu da sunadarin na da amfani wajen hana kamuwada cutar Korona amma ba hadiya ba.

Irin wannan ya faru a watan Afrilu inda wasu mutane suka fara hadiyan sunadarin tsaftace hannu sakamakon jawabin ba'a da shugaban kasa Amurka, Donald Trump, yayi cewa akwai yiwuwan shan sundarin zai iya hana kamuwa da cutar Korona.

Hudu sun mutu, 3 sun makance bayan shan sunadarin tsaftace hannu 'Hand Sanitizer'
Hudu sun mutu, 3 sun makance bayan shan sunadarin tsaftace hannu 'Hand Sanitizer'
Asali: Facebook

A bangare guda, Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 443 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:26 na daren ranar Juma'a 7 ga Agustan shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 443 da suka fito daga jihohin Najeriya 19 kamar haka:

Filato (103), Legas (70), Abuja (60), Ondo (35), Edo (27), Ribas (27), Kaduna (20), Osun (19), Borno (18), Oyo (18), Kwara (11), Adamawa (9), Nasarawa (7), Gombe (6), Bayelsa (4), Imo (4), Bauchi (2), Ogun (2) Kano (1).

An sallami mutum 32,637 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 936 a duk fadin kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel