Katsina: Yan sanda sun kashe yan bindiga 8, sun kwato shanu 30

Katsina: Yan sanda sun kashe yan bindiga 8, sun kwato shanu 30

Rundunar Ƴan sandan Jihar Katsina ta ce ta kashe wasu mutum takwas da ake zargin ƴan bindiga ne yayin wata arangama da suka yi a karamar hukumar Zamfarawa na jihar.

Ƴan sandan sun kuma ce sun kwato shanu guda 30 daga hannun ɓata garin kamar yadda Kakakin ƴan sanda SP Gambo Isah ya sanar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

"A ranar 06/08/2020 misalin ƙarfe 1 na rana, DPO na Batsari ya jagoranci tawagar "Operation Puff Adder" da "Sharan Daji" zuwa kauyen Zamfarawa a ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina sakamakon samun rahoton cewa ƴan bindiga fiye da 40 da bindigu AK-47 sun kai hari ƙauyen sun kashe wani Shafi'i Suleiman mai shekara 65 da Yakubu Idris mai shekara 70 kuma suka sace shanu da ba a tabbatar da adadin su ba.

Katsina: Yan sanda sun kashe yan bindiga 8, sun kwato shanu 30
Katsina: Yan sanda sun kashe yan bindiga 8, sun kwato shanu 30
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matar Ahmed Musa ta haifi ɗa namiji

"Tawagar ƴan sandan ta yi wa ƴan bindigan kwantar ɓauna a hanyar kauyen.

"Nan take tawagar ƴan sandan ta kashe ɗaya daga cikin ɓata garin yayin da sauran suka tsere cikin daji da raunin harsashi.

"Tawagar ta yi nasarar kwato shanu 30 daga cikin wadanda aka sace.

"Kazalika, a ranar 7/08/2020, wata tawagar cigiya ƙarƙashin jogorancin DPO da dagajin Zamfarawa sun sake gano gawarwakin ƴan bindiga bakwai a ƙauyen Barankada da ke ƙaramar hukumar Batsari na jihar Katsina," in ji shi.

Ya ce an gano kuɗi N22,300, harsashi, laya, makulli da takalma a tare da gawarwakin da aka gano yayin binciken.

A wani labarin, Shugaban Jami'ar Tarayya da ke Dutsin-Ma, Katsina, Farfesa Armaya'u Bichi, ya sanar da dakatar da duk ayyuka a mazaunin jami'ar na dindindin saboda fargabar hare-haren ƴan bindiga a ƙaramar hukumar.

Wannan umurnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa ta musamman mai ɗauke da sa hannun Direktan Hulda da Jama'a na Jami'ar, Habibu Matazu.

A cewar sanarwar, an umurci dukkan ma'aikatan jami'ar su dena zuwa mazaunin jami'ar na dindindin domin yin ayyuka a halin yanzu.

Umurnin ya fito ne ta ofishin rajistara, Alh. Dalha Kankia bayan rahotannin hare-haren ƴan bindiga a ƙauyukan da ke makwabtaka da jami'ar.

"Hakan yasa shugaban jami'ar dukkan ma'aikatan jami'ar da ke gudanar da ayyuka su koma mazaunin jami'ar na wucin gadi daga ranar Alhamis 6 ga watan Agusta.

"Za a sanar da mutanen da ke jami'ar ranar da za a cigaba da ayyuka a mazaunin jami'ar ta dindindin, " a cewar sanarwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel