Rashin tsaro: Daruruwan mutanen kudancin Kaduna sun gudu daga muhallansu

Rashin tsaro: Daruruwan mutanen kudancin Kaduna sun gudu daga muhallansu

-Al'ummar kudancin Kaduna sun fara guduwa daga muhallansu saboda tsoron harin yan bindiga dadi

- Sun fara barin mahaifarsu domin neman mafaka a wasu garuruwa

- Kakakin kungiyar al'ummar kudancin Kaduna SOKAPU, Luka Binniyat, ya bayyana haka

Gudun kada a sake kawo musu hari, daruruwan jama'an kudancin jihar Kaduna sun fara tashi daga muhallansu domin neman mafaka a wasu sassan jihar.

Luka Binniyat, Kakakin kungiyar al'ummar kudancin Kaduna SOKAPU, wanda ya bayyana hakan ya yi alhinin yadda rashin tsaro ke koron al'ummarsa daga mahaifarsu, The Guardian ta ruwaito.

A cewar Binniyat, SOKAPU yanzu na fuskantar kalubalen kula da yan gudun Hijra da hare-haren yan bindiga ya tilastawa guduwa daga gidajensu.

Ya ce tun bayan harin daren Laraba, mutanen na tsoron dawowan yan bindigan.

Rashin tsaro: Daruruwan mutanen kudancin Kaduna sun gudu daga muhallansu
Rashin tsaro: Daruruwan mutanen kudancin Kaduna sun gudu daga muhallansu
Asali: Twitter

Hare haren Kudancin Kaduna: Makarfi ya bukaci mazauna yankin su rungumi zaman lafiya

Mutane 33, yawanci yara mata da yara sun rasa rayukansu yayinda yan bindiga dadi suka sake kai hari kauyukan masarautar Atyap dake karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna.

Amma hukumar yan sanda ta ce mutane 21 aka kashe.

Daily Trust ta tattaro cewa hare-haren sun auku ne lokaci guda tsakanin karfe 11 na daren Laraba da karfe 1 na dare a kauyukan Apyiashyim, Atak’mawai, Kibori da Kurmin Masara a masarautar Atyap.

Wata majiya ta bayyana cewa saboda ruwan saman da akeyi, yan bindigan sun ci karansu ba babbaka duk da dokar ta bacin da gwamnatin ta sa.

Wani takardan da Kakakin kungiyar al'ummar kudancin Kaduna SOKAPU, Luka Biniyat, ya saki ya ce jama'an masarautar Atyap 33 aka kashe cikin kauyuka biyar: Apiojyim, Kibori, Apiako, Atakmawe da Magamiya.

Ya mika kokon baran kungiyar ga kasashen duniya a kawo musu dauki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel