Hare haren Kudancin Kaduna: Makarfi ya bukaci mazauna yankin su rungumi zaman lafiya

Hare haren Kudancin Kaduna: Makarfi ya bukaci mazauna yankin su rungumi zaman lafiya

Tsohon gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi ya yi kira ga mutanen Kudancin Kaduna su guji tashin hankali su rungumi sulhu.

Tsohon gwamnan ya nuna rashin jin dadin sa game da sake ɓarkewar rikici a yankin cikin sanarwar da kakakinsa Mukhtar Zubairu ya fitar ranar Juma'a.

Ya ce daukan doka a hannu don nuna bacin rai ƙara dagula lamura ya ke yi ba kawo maslaha ba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Hare haren Kudancin Kaduna: Makarfi ya bukaci mazauna yankin su rungumi zaman lafiya
Sanata Ahmed Makarfi. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Soja da ta yi ciki bayan ƴan bindiga sun mata fyade ta daukaka kara kan korarta daga aiki

"Ya yi imani cewa tattaunawa da juna ce hanya mafi dacewa na samar da tabatattaciyar zaman lafiya da fahimtar juna wacce ke kawo cigaba.

"A game da rikicin da ke faruwa a yankin, ya yi kira ga al'ummar su rungumi tattaunawa da juna da sulhu duk yadda ake ganin da wahala," in ji shi.

Ya kuma yi kira ga mutanen yankin su bawa gwamnati haɗin kai da goyon baya don magance wannan ƙallubalen.

Sanata Makarfi ya kuma yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya su tabbatar an tura isasun jami'an tsaro don samar da tsaro a yankin duba da cewa ana zargin wasu daga waje ne ke kai harin.

Ya shawarci hukumomi musamman gwamnatin jihar ta mayar da hankali wurin warware matsalar baki ɗaya ta hanyar neman hadin kan masu ruwa da tsaki kamar masu sarautar gargajiya da shugabannin addini, ƴan siyasa da shugabannin al'umma.

Makarfi ya kuma mika sakon ta'aziyar sa ga iyalan wadanda rikicin ya shafa da gwamnatin Kaduna da daukakin al'ummar jihar.

A wani labarin, Kungiyar gwamnonin Arewa, NGF, a ranar Alhamis ta yi tir da harin da aka kai a Kudancin Kaduna a baya bayan nan inda aka kashe kimanin mutum 22 a daren ranar Laraba.

Shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau cikin sanarwar da direktan watsa labaransa, Dr Makut Macham ya fitar ya bayyana harin a matsayin abin bakin ciki.

Ya nuna damuwarsa kan yadda har yanzu ba a riga an kamo yan bindigan da suka kai harin a kauyukan Atyap guda hudu a karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.

Ya ce hare haren da aka kai wa kauyukan ya nuna cewa baya ga zaluntar mazauna kauyen da suke yi, bata garin sun dage domin ganin sun dakile kokarin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi don samar da zaman lafiya.

"Muna bakin cikin afkuwar hare haren da zubar da jinin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Muna Allah wadai da hakan.

"A yayin da muke kira ga hukumomin tsaro su kare dage wa don kama bata garin, muna kira ga mazauna yankunan su taimakawa jamian tsaro da bayannan sirri da zai taimaka a kama bata garin," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel