Ku tilasta wa al'umma sanya takunkumin rufe fuska - Buhari ya gargadi gwamnoni

Ku tilasta wa al'umma sanya takunkumin rufe fuska - Buhari ya gargadi gwamnoni

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya hori gwamnonin fadin tarayya da su tabbatar sun tilasta sanya takunkumin rufe fuska a tsakanin al'ummominsu a wani mataki na dakile bazuwar annobar korona.

Gargadin shugaban kasar ya zo ne a ranar Laraba bayan karbar rahoto daga fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona wanda sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya ke jagoranta.

Sai dai a yayin mika wa shugaba Buhari rahoton, sakataren gwamnatin ya ce ana samun ci gaba a fagen yaki da cutar korona da ake ci gaba da yi a fadin kasar.

Mista Mustapha ya ce a saurari bayani kan matakin da cutar take nan ba dadewa tare da sanar da mataki na gaba za a daukar mata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 443 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:26 na daren ranar Juma'a 7 ga Agustan shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 443 da suka fito daga jihohin Najeriya 19 kamar haka:

Filato (103), Legas (70), Abuja (60), Ondo (35), Edo (27), Ribas (27), Kaduna (20), Osun (19), Borno (18), Oyo (18), Kwara (11), Adamawa (9), Nasarawa (7), Gombe (6), Bayelsa (4), Imo (4), Bauchi (2), Ogun (2) Kano (1).

KARANTA KUMA: Gawurtaccen ɗan daba ya shiga hannun 'yan sanda a Kano

An sallami mutum 32,637 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 936 a duk fadin kasar.

Bayan fiye da watanni hudu da bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu a jihohi 36 da kuma babban babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.

Rumbun tattaro bayanai na NCDC ya nuna cewa, an yi wa mutum 310,729 gwajin cutar kuma an tabbatar da harbin mutum 45,687 a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel