Gawurtaccen ɗan daba ya shiga hannun 'yan sanda a Kano

Gawurtaccen ɗan daba ya shiga hannun 'yan sanda a Kano

Wani fitaccen dan daba da ya gawurta mai suna Aminu A. Aminu, ya shiga hannun jami'an tsaro na 'yan sanda a birnin Kanon Dabo.

Kafar watsa labarai ta Gidan Rediyon Freedom ta ruwaito cewa, Aminu mai shekaru 21 a duniya ya fada tarkon jami'an tsaro bayan ya aikata mummunar ta'asa a baya bayan nan.

An ruwaito cewa, Aminu ya kasance fittacen dan sara suka da ya addabi al'ummar Unguwannin Kwalli da Sagagi da ke karkashin karamar Hukumar birni a Kano.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai.

Jami'an 'yan sanda a bakin aiki
Hoto daga jaridar Premium Times
Jami'an 'yan sanda a bakin aiki Hoto daga jaridar Premium Times
Asali: Twitter

DSP Kiyawa ya ce mutumin da ake zargi ya shiga hannu ne bayan sun samu korafi daga wani matashi mai shekaru 31 mazaunin unguwar Sagagi, Mubarak Abdul, wanda ya shigar da karar cewa Aminu ya kafta masa sara da wuka a wuya.

Kamar yadda babban jami'in dan sandan ya bayyana, nan da nan a ka garzaya da shi asibitin Murtala yayin da ake ci gaba da bincike domin gurfanar da wanda ake zargi a gaban Kuliya.

A wani rahoton Legit.ng ta ruwaito cewa, wani fusataccen mahaifi ya yanke wa dan cikinsa haddi saboda zargin tarayya da kungiyar asiri a garin Nyangansang da ke Calabar a Jihar Kuros Riba.

Sunday Brown mazaunin yankin Nyomidibi ya guntule wa dan sa Mathewa ya shiga kungiyar asiri.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis bayan Mista Brown da dansa, Mathew, sun yi fito-na-fito kamar yadda su ka saba.

KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 110 a Zamfara

Wani makwabcin Mista Brown ya shaidawa manema labarai cewa rigimar da ke tsakanin uba da ‘da ta fara zama barazana ga mazauna unguwar, saboda yanzu haka abokan matashin sun fara barazanar daukan fansa.

Majiyar ta bayyana cewa shigar Mathew kungiyar tsafi da sauran halayensa na gagara sune suka jawo mahaifinsa ya datse ma sa hannu.

Wani shugaba a unguwar, Timothy Sam, ya shaidawa manema labarai cewa jami'an 'yan sanda sun sha kama Mathew saboda gagararsa da kuma yawon dare mai cike da alamun tambaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel