Jami'ar KUST Wudil ta daga likafar malamai 17 zuwa furofesoshi

Jami'ar KUST Wudil ta daga likafar malamai 17 zuwa furofesoshi

Majalisar da ke sa ido kan al’amuran gudanarwa a jami’ar kimiya da fasaha ta jihar Kano da ke Wudil, ta amince da yi wa malamanta 17 karin girma zuwa matsayin furofesa.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Abdullahi Datti, mataimakin shugaban yada labarai da hulda da al’umma ya fitar a ranar Juma’a.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, jami’ar ta ba da lamunin daga likafar malaman yayin zaman majalisar gudanarwarta karo na 50 da aka gudanar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa ba da lamunin yin karin girman ya biyo bayan tantance lakcarorin da abin ya shafa.

Jami'ar KUST Wudil
Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Jami'ar KUST Wudil Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Asali: Twitter

Mista Datti ya kara da cewa, bayanan tantancewar sun nuna cewa an daga matsayin malamai 6 zuwa matakin furofesa, yayin da ragowar 11 aka daga likafarsu zuwa matsayin na kusa da furofesa wato associate.

A cewarsa, malaman da suka zama Furofesoshi sun hada da Nuruddeen Umar; Olu Adeshola, Alhassan Musa, Sani Muhammad, Abubakar Musa da Ado Bichi.

Mista Datti ya kuma jeranto sunayen wanda aka ba mukamin na kusa da furofesa sun hadar da; Sa’ad Muhammad, Maitama Abubakar, Umar Ibrahim, Sanusi Yakubu, da Hassan Jamo.

Sauran sun hada da; Muhammad Alhaji, Nuruddeen Muhammad, Ado Abdu, Murtala Dambatta, Mahdi Lawan da Abdullahi Dawakin-Kudu.

Shugaban jami’ar Farfesa Shehu Musa, a cikin sakonsa na taya murna, ya nemi malaman da suka samu karin girma a kan su dage wajen nazari da binciken ilimi da zai kara daga darajar jami’ar da haska ta a idon duniya.

KARANTA KUMA: Obaseki ya musanta zargin bayar da kwangiloli ta hanyar da ba ta dace ba

A wani rahoton Legit.ng ta ruwaito cewa, Farfesa Sagir Aminu Abbas, ya doke sauran abokan takararsa a zaben al'ummar jami'a, wani babban mataki na neman zama shugaban jami'ar Bayero dake jihar Kano.

Farfesa Sagir Abbas, wanda tsohon mataimakin shugaban jami'ar ne, ya samu kuri'u 1,026 inda ya doke wanda ke biye da shi, Farfesa Adamu Idris Tanko, mai kuri'u 416.

Rahotanni sun bayyana cewa, bisa al'adar jam'iar, duk wanda ya lashe zaben a wannan mataki da Farfesa Sagir ya yi nasara, shi ne ke zama shugaban jami'ar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel