Katsina: Fargabar harin ƴan bindiga yasa an rufe jami'ar Tarayya ta Dutsin-Ma
Shugaban Jami'ar Tarayya da ke Dutsin-Ma, Katsina, Farfesa Armaya'u Bichi, ya sanar da dakatar da duk ayyuka a mazaunin jami'ar na dindindin saboda fargabar hare-haren ƴan bindiga a ƙaramar hukumar.
Wannan umurnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa ta musamman mai ɗauke da sa hannun Direktan Hulda da Jama'a na Jami'ar, Habibu Matazu.
A cewar sanarwar, an umurci dukkan ma'aikatan jami'ar su dena zuwa mazaunin jami'ar na dindindin domin yin ayyuka a halin yanzu.

Asali: Twitter
"Umurnin ya fito ne ta ofishin rajistara, Alh. Dalha Kankia bayan rahotannin hare-haren ƴan bindiga a ƙauyukan da ke makwabtaka da jami'ar.
"Hakan yasa shugaban jami'ar dukkan ma'aikatan jami'ar da ke gudanar da ayyuka su koma mazaunin jami'ar na wucin gadi daga ranar Alhamis 6 ga watan Agusta.
"Za a sanar da mutanen da ke jami'ar ranar da za a cigaba da ayyuka a mazaunin jami'ar ta dindindin, " a cewar sanarwar.
DUBA WANNAN: An kama dagajin ƙauye da ke haiƙe wa ƴarsa mai shekara 15
A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa ana cigaba da kai hare hare a jihar a sassa daban daban.
A ranar Laraba, Gwamna Aminu Masari ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari inda ya yi masa bayanin halin da jihar ke ciki.
Da ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnati bayan ganawa da shugaban kasa, gwamnan ya ce ana iya ƙoƙarin ganin an magance ƴan bindigan amma suna yi wa shirin noma na gwamnati cikas.
"Tabbas, za a samu wasu matsaloli, saboda a jihar baki daya, rikicin ƴan bindigan ya shafi kananan hukumomi tara cikin 34," a cewar Masari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng