Ba ma cusa Dala cikin Aljihu a Edo - Obaseki ya mayarwa Ganduje martani

Ba ma cusa Dala cikin Aljihu a Edo - Obaseki ya mayarwa Ganduje martani

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya mayarwa gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje martani mai zafi don ya ce babu aikin a zo a ganin da yayiwa al'ummar Edo.

Yayinda yake magana a fadar shugaban kasa ranar Juma'a, Ganduje wanda shine shugaban kwamitin yakin neman zaben APC a jihar Edo ya ce gazawar Obaseki zai saukaka musu wajen samun nasara a zaben ranar 19 ga Satumba.

Amma martani kan jawabin Ganduje, mai magana da yawun Obaseki, Crusoe Osagie , ya ce Ganduje bai da alhakin auna kokarin Obaseki saboda "irin bidiyon da ya bayyana kansa yana cusa Dalan da ya karba daga yan kwangila."

Jawabin yace: "Maganar da gwamna Ganduje yayi kan kokarin Obaseki a ofis abin dariya ne. Hakazalika abin kunya ne saboda APC ta gaza fahimtar abinda ake nufi da kokari saboda irin namijin kokarin da gwamna Obaseki yayi a bangarori daban-daban ya sanya soyayyarsa cikin zukatan mutan jihar Edo."

"Babu irin kananan maganganun da APC da masu yakin neman zabenta zasuyi da zai goge ayyukan da suka bazu a lunguna da sakon jihar Edo."

"Ganduje bai da hakkin auna kokarin gwamna Obaseki ko wani gwamna saboda yanada kashi a gindi, wanda yake bukatar wankewa."

Ba ma cusa Dala cikin Aljihu a Edo - Obaseki ya mayarwa Ganduje martani
Ba ma cusa Dala cikin Aljihu a Edo - Obaseki ya mayarwa Ganduje martani
Asali: Facebook

A bangare guda, Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na kasa, Abubukar Malami, ya baiwa Sifeto Janar na hukumar yan sanda ya samar da kariya da tsaro wa yan majalisar dokokin jihar Edo na jam'iyyar All Progressives Congress APC 17.

A wasikar da ya aike masa ranar 5 ga Agusta bisa wani kara da lauyan yan majalisar, West Idahosa, ya shigar, Malami ya ce akwai bukatar bada tsaro domin hana barkewar rikici a Edo.

Yan majalisan 17 dake goyon bayan dan takaran jam'iyyar APC, Fasto Osaze Ize-Iyamu, sun kasance cikin rikici da takwarorinsu bakwai dake goyon bayan gwamnan jihar Godwin Obaseki.

A jiya mun kawo muku rahoton cewa 'yan majalisu 17 na majalisar dokokin jihar Edo, da suka hada da mambobi 12 da a baya aka bayyana kujerarsu a matsayin wofi, sun yi ikirarin cewa sun tsige kakakin majalisar jihar, Francis Okiye, da mataimakinsa, Roland Asoro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel