NUPENG ta umurci mambobinta na Legas su tafi yajin aiki

NUPENG ta umurci mambobinta na Legas su tafi yajin aiki

Kungiyar masu dakon mai da iskar gas, NUPENG, ta umurci mambobinta su dena aiki a Legas daga ranar Litinin kamar yadda umurni daga shugabannin kungiyar ya zo.

NUPENG, a ranar Juma'a ta ce an dauki wannan matakin ne saboda an gaza magance wasu manyan matsaloli uku direbobin ke fuskanta na tsawon watanni uku.

Shugaban Kungiyar Williams Akporeha da sakataren kungiyar, Olawale Afolabi, ne suka bayar da umurnin kamar yadda The Nation ta ruwaito.

NUPENG ta umurci direbobin tanka na Legas su tafi yajin aiki
NUPENG ta umurci direbobin tanka na Legas su tafi yajin aiki. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama dagajin ƙauye da ke haiƙe wa ƴarsa mai shekara 15

Sanarwar ta ce, "Shugabanni da mambobin kungiyar mu na cikin baƙin ciki da damuwa saboda kalubalen da direbobin man fetur ɗin mu na Legas ke fuskanta.

"A halin yanzu ba mu da wani zaɓi da ya rage mu janye ayyukan mu a Legas har sai lokacin da gwamnatin Legas da masu ruwa da tsaki suka magance matsalolin.

"Abin takaici ne yadda muka yi ta yin korafi da tunatarwa ga gwamnatin jihar Legas da kwamitin shugaban kasa na yaƙi da corona su rage cinkoson da ke tashar Apapa amma hakan bai yi wu ba.

"Mun yanke shawarar zuwa yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin, 10 ga watan Agustan 2020, karfe 12 na dare idan har gwamantin jihar Legas ba ta magance matsalolin da muke fama da su ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel