Yanzu-yanzu: Antoni Janar ya baiwa IGP umurnin bada kariya ga yan majalisan Edo mabiya Oshiomole 17

Yanzu-yanzu: Antoni Janar ya baiwa IGP umurnin bada kariya ga yan majalisan Edo mabiya Oshiomole 17

Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na kasa, Abubukar Malami, ya baiwa Sifeto Janar na hukumar yan sanda ya samar da kariya da tsaro wa yan majalisar dokokin jihar Edo na jam'iyyar All Progressives Congress APC 17.

A wasikar da ya aike masa ranar 5 ga Agusta bisa wani kara da lauyan yan majalisar, West Idahosa, ya shigar, Malami ya ce akwai bukatar bada tsaro domin hana barkewar rikici a Edo.

Yan majalisan 17 dake goyon bayan dan takaran jam'iyyar APC, Fasto Osaze Ize-Iyamu, sun kasance cikin rikici da takwarorinsu bakwai dake goyon bayan gwamnan jihar Godwin Obaseki.

Yanzu-yanzu: Antoni Janar ya baiwa IGP umurnin bada kariya ga yan majalisan Edo mabiya Oshiomole 17
Wasikar
Asali: UGC

KU KARANTA: Edo: Ku kiyayi irin abinda ya faru a Zamfara da Rivers - Buhari ya gargadi Ganduje, Bagudu da Buni

A jiya mun kawo muku rahoton cewa 'yan majalisu 17 na majalisar dokokin jihar Edo, da suka hada da mambobi 12 da a baya aka bayyana kujerarsu a matsayin wofi, sun yi ikirarin cewa sun tsige kakakin majalisar jihar, Francis Okiye, da mataimakinsa, Roland Asoro.

Sun yanke wannan hukuncin ne a ranar Alhamis a wani boyayyen wuri a Benin City, babban birnin jihar, awanni bayan da jami'an tsaro suka mamaye zauren majalisar.

A bangarensu, sunce sun nada Victor Edoror, mai wakiltar mazabar Esan ta tsakiya, da Emmanuel Agabje, daga mazabar Akoko-Edo II a matsayin kakakin majalisar da mataimakinsa.

A wajen taron, 'yan majalisu 12 da aka zabe su, an rantsar da su tare da sauran 'yan majalisun 5 wadanda suka yi mubayi'a ga Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC, suka ce sun tsige kakakin.

Majalisar dokokin jihar Edo ta kasance cikin rikici tun a shekarar 2019, wacce ta sake rikicewa a yanzu a yayin da ake shirye shiryen zaben gwamnan jihar.

An zabi 'yan majalisu 24 daga mazabu 24 na jihar a babban zaben 2019. Sai dai, 10 daga cikinsu, an rantsar da su ne a ranar 17 ga watan Yulin shekarar, lamarin da ya jawo zaune-tsaye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel