Yan sanda sun kama Manjo ɗin Soja na bogi ɗauke da wiwi masu yawa (Hotuna)

Yan sanda sun kama Manjo ɗin Soja na bogi ɗauke da wiwi masu yawa (Hotuna)

Jami'an ƴan sanda na musamman na Safer Highways a jihar Delta sun kama wani Manjo ɗin Soja na bogi, Ojumah, wanda ake ce yana safarar ganyen wiwi.

Fabian, mai shekaru 44 ɗan asalin garin Abbi ne daga karamar hukumar Ndokwa-West a jihar Delta.

Wani sanarwar da ƴan sanda suka wallafa a dandalin sada zumunta a ranar Juma'a ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Juma'a 31 ga watan Yunin 2020 a Benin.

Yan sanda sun kama Manjo ɗin Soja na bogi dauke da wiwi (Hotuna)
Yan sanda sun kama Manjo ɗin Soja na bogi dauke da wiwi (Hotuna). Hotuna daga LIB
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama dagajin ƙauye da ke haiƙe wa ƴarsa mai shekara 15

A cewar sanarwar, an kuma kwato motar sojoji mai lamba NA142-B01 dauke da ganyen wiwi kanton 420 daga wurin wanda ake zargin.

Yan sanda sun kama Manjo ɗin Soja na bogi dauke da wiwi (Hotuna)
Yan sanda sun kama Manjo ɗin Soja na bogi dauke da wiwi (Hotuna). Hotuna daga LIB
Asali: Twitter

Wanda ake zargin, Fabian, ya ce ya fara harkar safarar ganyen wiwi ɗin tun shekarar 2014.

Rahoton ya kuma ce ya amsa cewa motar tasa ne kuma ya siya lambar sojojin ne daga hannun wani soja.

Yan sanda sun kama Manjo ɗin Soja na bogi dauke da wiwi (Hotuna)
Yan sanda sun kama Manjo ɗin Soja na bogi dauke da wiwi (Hotuna). Hotuna daga LIB
Asali: Twitter

Kazalika, ya kuma ce ya siyo kayan sojojin daga kasuwar Mammy a wani barikin soja.

An kuma gano cewa akwai yiwuwar "ya girma a barikin soja ne kuma ya taɓa samun horo da ta yi kama da na sojoji duk da cewa shi ba soja bane."

A wani labarin, a kalla mutum 20 ne suka riga mu gidan gaskiuya kuma wasu da dama suka jikatta sakamakon sabbin hare haren da aka kai a wasu garuruwa uku a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce ana zargin yan daba ne suka kai harin da ya faru a ranar Alhamis kamar yadda Channels TV ta ruwaito. Garruruwan da aka kai harin sun hada da Kurmin Masara, Apyia Shyim, and Takmawai .

Wannan sabbin harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan an tura jami'an tsaro zuwa wasu garruruwan da ake ganin sun cikin hatsari ko kuma rikici na iya barkewa.

Sufeta Janar na Yan sanda, Mohammed Adamu ya umurci kwamishinan yan sandan jihar ya tura jamiansa domin kare rayuka da dukiyoyin mutanen garuruwan da abin ya shafa.

Rundunar yan sanda ba ta tabbatar da harin ba amma shugaban karamar hukumar Zangon Kataf, Elias Manza ya shaidawa Channels Television cewa wasu yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kai hari a garuruwan uku da asubahin ranar Alhamis suna harbe harbe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel