Matan jam'iyyar PDP sun yi zanga-zanga a Majalisar Edo

Matan jam'iyyar PDP sun yi zanga-zanga a Majalisar Edo

Mambobin Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, reshen mata a ranar Juma'a sunyi zanga-zangar nuna goyon baya ga Kakakin Majalisar da aka tsige.

An dai tsige Mr Frank Okiye ne a kan zarginsa da haɗin baki da wasu ƴan jam'iyyar APC don kwace iko a majalisar ba bisa ka'ida ba.

Matan sun fara tattaki ne daga gidan gwamanti jihar da ke Osadebey Avenue zuwa Anthony Shagari Complex da ke Ring Road don nuna goyon bayan su ta Okiye.

Matan jam'iyyar PDP sun yi zanga-zanga a Majalisar Edo
Matan jam'iyyar PDP sun yi zanga-zanga a Majalisar Edo. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya tafi Senegal don hallartar jana'izar ɗan Sheikh Inyass

Rahotanni sun bayyana cewa an tsige Okiye ne a ranar Alhamis inda 17 cikin ƴan majalisar 24 suka haɗu a wani gida a Benin a bayan idonsa suka tsige shi suka naɗa sabon kakaki, Mr Victor Edoror.

Wasu daga cikin matan da suka yi ikirarin cewa suna da asiri sun yi tsinuwa a kofar shiga harabar Majalisar.

Sunyi Allah wadai da tsige Okiye da ƴan majalisar jihar 17 suka yi a ranar Alhamis kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ku saurari ƙarin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel