Rashin tsaro: Ku kiyayi zuwa Kano, Kaduna, Katsina da wasu jihohi 16 - Birtaniya ta gargadi yan kasarta dake Najeriya

Rashin tsaro: Ku kiyayi zuwa Kano, Kaduna, Katsina da wasu jihohi 16 - Birtaniya ta gargadi yan kasarta dake Najeriya

Gwamnatin Birtaniya ta shawarci yan kasarta dake zaune a Najeriya su kiyayi zuwa wasu jihohi yankunan Arewa maso gabas, Arewa maso yamma da Kudu maso kudancin Najeriya.

Birtaniya ta bayyana cewa ta na bada wannan shawara ne saboda irin matsalar tsaron da ake fuskanta a jihohin.

Jihohin sune; Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Kaduna, Kano, Bauchi, Niger, Jigawa, Katsina, Zamfara, Kogi, Abia da Rivers.

Sauran sune Delta, Bayelsa, Akwa Ibom da Cross River.

Birtaniya ta bayyana wannan shawara ne a shafinta na yanar gizo inda tace "Ofishin wajen Birtaniya tana shawartan yan kasar Birtaniya kan zuwa wuraren nan sai dai idan akwai muhimmanci sosai"

Rashin tsaro: Ku kiyaye zuwa Kano, Kaduna, Katsina da wasu jihohi 16 - Birtaniya ta gargadi yan kasarta dake Najeriya
Firam Ministan Birtaniya
Asali: UGC

KU KARANTA: An kashe sabbin mutane 33 a kudancin Kaduna

Takardan ya kara da cewa rashin tsaro ya sabbabawa kasar rage yawan ma'aikatanta dake ofishin jakadancinta dake Abuja da Legas.

Ofishin jakandancin Birtanya ta kara da cewa an samu rahoton yan ta'addan Al-Qa'ida sun fara kai hare-hare a jihar Kaduna.

"An kaiwa kungiyoyin tallafi hare-hare a Arewa maso gabas, Monguno a jihar Borno ranar 13 ga Yuni, 2020."

"Hakazalika an kai wasu hare-hare Gombe, Kano Kaduna, Jos, Bauchi, da birnin tarayya." Ofishin ta yi gargadi.

A bangare guda, Hedkwatan tsaron Najeriya ta ce labarin cewa yan kungiyar Al-Qa'ida sun fara shiga yankin yammacin nahiyar Afrika ba sabon abu bane.

Jagoran sashen yada labaran hukumar, Manjo Janar John Enenche, ya ce tuni suna sane da hakan.

Enenche ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai ranar Alhamis a Abuja yayinda yake tsokaci kan maganar kwamandan Sojin Amurka, Manjo Janar Dagvin Anderson.

Ya ce kawai Sojan Amurkan ya yi kira da hukumar Sojin Najeriya ta cigaba da ruwan wutan da take yiwa yan ta'addan Boko Haram da abokansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel