Rundunar 'yan sanda ta cafke masu garkuwa da mutane 45 da suka addabi Borno

Rundunar 'yan sanda ta cafke masu garkuwa da mutane 45 da suka addabi Borno

- Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta cafke mutane 45 da ake zarginsu da laifin garkuwa da mutane

- Jihar Borno ta dade tana fuskantar matsalolin tsaro, inda aka kashe mutane da dama, ya yin da dubunnai suka rasa muhallansu na gado

- Rundunar ta tabbatar da cewa za a yanke hukunci ga wadanda aka tabbatar sun aikata laifin da zaran ta kammala bincike

Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta cafke mutane 45 da ake zarginsu da laifin garkuwa da mutane da mallakar miyagun makamai a sassa daban daban na jihar.

Daga cikin wadanda aka kama, akwai mai shekaru 40 wanda ake zargin ya kware wajen safarar makamai ga 'yan ta'addan Boko Haram.

Jihar Borno ta dade tana fuskantar matsalolin tsaro, inda aka kashe mutane da dama, ya yin da dubunnai suka rasa muhallansu na gado.

A yayin da jami'an tsaro ke fafutukar dai-daita lamuran tsaro a jihar, a hannu daya kuma ana aikata wasu laifukan a sassa daban daban na jihar.

Amma rundunar 'yan sanda ta jihar Borno ta ce ba za ta sarara ba har sai ta wanzar da zaman lafiya da cafke masu aikata munanan laifuka a jihar.

Wadanda ake zargin, an cafkesu ne da laifin garkuwa da mutane, kisan kai, fashi da makami da sauran wasu ayyukan ta'addanci.

KARANTA WANNAN: Ka janye sunan Jonathan da Awolowo da ka sanyawa tashoshin layin dogo - Clark ga Buhari

Karshen alewa kasa: An cafke masu garkuwa da mutane 45 a jihar Borno
Karshen alewa kasa: An cafke masu garkuwa da mutane 45 a jihar Borno
Asali: UGC

Wasu daga cikin wadanda aka cafken, da suka zanta da gidan talabijin na TVC News, sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da su.

Rundunar ta tabbatar da cewa za a yanke hukunci ga wadanda aka tabbatar sun aikata laifin da zaran rundunar ta kammala gudanar da bincike a kansu.

A hannu daya kuwa; Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa na kan turbarta na yaki da cin hanci da rashawa, da yiwa dukiyar al'umma zagon kasa.

Shugaban kasar ya yi wannan bayani ne a taron bukin yaye daliban aji 28 na kwalejin tsaro ta kasa a ranar Alhamis a Abuja.

KARANTA LABARIN: Babban shirin da nayi na kawo karshen cin hanci da rashawa a Nigeria - Shugaba Buhari

Da ya samu wakilcin ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce har yanzu akwai sauran aiki wajen farfado da tattalin arzikin kasa, kamar daukar aiki, kawar da talauci da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel