Turmi da tabarya na kama shi da diyarsa, shiyasa na rabu da shi - Matar basarake

Turmi da tabarya na kama shi da diyarsa, shiyasa na rabu da shi - Matar basarake

Jami'an 'yan sanda a jihar Ogun sun damke dagacin kauye, Rasheed Sholabi, a kan zarginsa da ake da lalata diyar cikinsa mai shekaru 15.

Sholabi na da sarautar Baale of Oose Agbedu Ajibawo a yankin Owode-Yewa da ke karamar hukumar Yewa ta Kudu ta jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

An gano cewa 'yan sandan sun kama dagacin ne bayan rahoton da diyarsa, wacce ta shiga ofishin 'yan sanda da ke Owode Egbado ta kai.

Ta sanar da cewa mahaifinta yana lalata da ita tun tana karamarta.

A wata takarda da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya fitar a jiya a Abeokuta, ya ce yarinyar da bakinta ta sanar da cewa mahaifinta ya fara lalata da ita tun tana da shekaru 11.

Yarinyar tace, tana da babbar matsala da mafitsararta saboda abinda mahaifinta yake mata.

"Yarinyar ta sanar da 'yan sanda cewa mahaifiyarta ta rasu tun kafin ta kai shekaru biyu kuma mahaifinta ya hana kowa daukarta," Oyeyemi yace.

Kakakin ya ce, bayan wannan korafin, SP Olabisi Elebute, ya jagoranci jami'ansa don kama Sholabi.

Ya fara musanta zargin a farko amma har suma sai da yayi yayin da diyarsa ta tsaya gabansa kuma aka tabbatar da an samu shaida daga tsohuwar matarsa.

Turmi da tabarya na kama shi da diyarsa, shiyasa na rabu da shi - Matar basarake
Turmi da tabarya na kama shi da diyarsa, shiyasa na rabu da shi - Matar basarake. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jarumta: 'Yan kauye sun yi wa 'yan bindiga mugun duka, sun kashe daya a Katsina

"Tsohuwar matarsa ta sanar da 'yan sanda cewa ta kama shi turmi da tabarya yana lalata da diyarsa kuma wannan dalilin ne yasa ta tsere ta bar shi," Oyeyemi yace.

Ya ce an mika yarinyar gidan marayu don kula da ita.

Oyeyemi ya kara da cewa, kwamishinan 'yan sandan jihar Ogun, Edward A. Ajogun, ya bukaci a mika lamarin gaban sashen bincike a kan cin zarafin kananan yara da safararsu.

A wani labari na daban, wata malamar makaranta mai suna Iyabo Amusan a ranar Alhamis, ta garzaya gaban wata kotun gwargajiya da ke Mapo inda ta bukaci alkali da ya raba ta da mijinta saboda tsananin fushinsa.

Kamar yadda Iyabo ta sanar, ta ce ta amince da barin 'ya'yan a hannun Joseph amma in har za ta rabu da shi tare da samun kariya a rayuwarta.

"Joseph ya saba bata min suna tare da kirana macuciya.

"Mai shari'a, ban san me yasa Joseph ya yanke hukuncin tozarta ni da ci min mutunci ba. A kowacce rana, rigima ta daban ce a gida na.

"Duk lokacin da ya dukeni, yana min tsirara. Yana zargina da mallakar kwalin bogi wanda na samu aiki da shi.

"Mummunan kudirin Joseph a kaina shine ganin bayana. Ya taba sassara ni da adda inda nayi doguwar jinya a asibiti.

"Duk da haka, baya bani abinci tare da 'ya'yana. Ina biyan haya da kaina," Iyabo tace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: