Ba wani sabon abu ne, mun sani - Hukumar Sojin Najeriya ta mayarwa Amurka martani kan shigan yan ta'adda Arewa maso yamma

Ba wani sabon abu ne, mun sani - Hukumar Sojin Najeriya ta mayarwa Amurka martani kan shigan yan ta'adda Arewa maso yamma

- Mai magana da yawun jami'an tsaron Najeriya ya yi watsi da sakon Sojin Amurka kan shigan yan ta'adda Afrika ta yamma

- Enenche ya ce tuni suna da labarin hakan kuma ba sabon abu bane

Hedkwatan tsaron Najeriya ta ce labarin cewa yan kungiyar Al-Qa'ida sun fara shiga yankin yammacin nahiyar Afrika ba sabon abu bane.

Jagoran sashen yada labaran hukumar, Manjo Janar John Enenche, ya ce tuni suna sane da hakan.

Enenche ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai ranar Alhamis a Abuja yayinda yake tsokaci kan maganar kwamandan Sojin Amurka, Manjo Janar Dagvin Anderson.

Ya ce kawai Sojan Amurkan ya yi kira da hukumar Sojin Najeriya ta cigaba da ruwan wutan da take yiwa yan ta'addan Boko Haram da abokansu.

Ba wani sabon abu ne, mun sani - Hukumar Sojin Najeriya ta mayarwa Amurka martani kan shigan yan ta'adda Arewa maso yamma
Hukumar Sojin Najeriya ta mayarwa Amurka martani kan shigan yan ta'adda Arewa maso yamma
Asali: Twitter

Ranar Talata, Gwamnatin kasar Amurka ta bayyanawa duniya cewa mambobin kungiyar yan ta'addan Al-Qa'ida sun fara ratsawa jihohin Arewa maso yammacin Najeriya.

Kwamandan Sojin Amurka na harkoki na musamman a nahiyar Afrika, Dagvin Anderson, wanda ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai ya ce kungiyar na shiga wurare daban-daban a yammacin Afrika.

Jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sune: Kaduna, Kano, Katsina, Jigawa, Zamfara, Kebbi, da Sokoto.

Amma Enenche a martaninsa ya ce hukumar Sojin Najeriya bata jahilci hakan ba saboda Sojojin Najeriya ne suka nabbahar da duniya cewa yan ta'adda sun fara shiga yankin Afrika ta yamma.

Yace: "A nawa, wannan ba shi bane karo na farko da suka fadin haka; an kai shekaru biyar ko goma ana fada kuma hukumar Sojin kasar nan na sane."

A bangare guda, Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa wasu dinbin ‘tan ta’addan kungiyar Boko Haram na bangaren Abubakar Shekau, sun fitar da sabon bidiyo na musamman.

‘Yan ta’addan da su ka yi wa Abubakar Shekau mubaya'a sun ce sun dauki wannan bidiyo ne a jihar Neja da ke a yankin Arewa maso tsakiyar kasar.

Malam Audu Bulama Bukarti, wani masanin harkar tsaro ya bayyana wannan a shafinsa na Twitter dazu. A wannan bidiyo an ga mutane kimanin dari su na gabatar da sallar idi a kungurmin daji.

Daga baya wasu mayaka sun yi magana ne da harshen Hausa, Ingilishi da kuma Fulfulde.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel