Gwamnonin Arewa na duba yiwuwar yin sulhu da 'yan bindiga - Gwamnan Sokoto

Gwamnonin Arewa na duba yiwuwar yin sulhu da 'yan bindiga - Gwamnan Sokoto

Gwamnonin Arewa maso Yamma suna duba yiwuwar yin sulhu da 'yan bindiga na nufin kawo karshen kallubalen tsaro da ake fama da shi a yankin.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai wa takwararsa na jihar Zamfara, Bello Matawalle.

Hare haren yan bindiga, satar shanu da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ta kazanta a jihohin Zamafara da Sokoto a baya bayan nan.

Gwamnonin Arewa na duba yiwuwar yin sulhu da yan bindiga - Tambuwal
Gwamnonin Arewa na duba yiwuwar yin sulhu da yan bindiga - Tambuwal
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Soja da ta yi ciki bayan ƴan bindiga sun mata fyade ta daukaka kara kan korarta daga aiki

Yin sulhu da yan bindigan ya haifar da sakamako mai kyau a cewar gwamnan Zamfara Bello Matawalle kamar yadda TVC News ta ruwaito.

Akwai yiwuwar gwamnonin Arewa maso Yamma su dauki wannan matakin domin kawo karshen hare haren 'yan bindiga, garkuwa da mutane da satar shanu a yankin.

Tsohon gwamnan Zamfara, Mamuda Shinkafi ya yabawa kokarin da gwamna Matawalle ya yi na magance kallubalen tsaro a jihar.

Ya yi imanin cewa sauya shugabannin hukumomin tsaro ba shine abinda ya fi dace wa ba a wannan lokacin da ake cikin tsaka mai wuya.

A wani labarin, a kalla mutum 20 ne suka riga mu gidan gaskiya kuma wasu da dama suka jikatta sakamakon sabbin hare haren da aka kai a wasu garuruwa uku a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce ana zargin yan daba ne suka kai harin da ya faru a ranar Alhamis kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Garruruwan da aka kai harin sun hada da Kurmin Masara, Apyia Shyim, and Takmawai .

Wannan sabbin harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan an tura jami'an tsaro zuwa wasu garruruwan da ake ganin sun cikin hatsari ko kuma rikici na iya barkewa.

Sufeta Janar na Yan sanda, Mohammed Adamu ya umurci kwamishinan 'yan sandan jihar ya tura jami'ansa domin kare rayuka da dukiyoyin mutanen garuruwan da abin ya shafa.

Rundunar yan sanda ba ta tabbatar da harin ba amma shugaban karamar hukumar Zangon Kataf, Elias Manza ya shaidawa Channels Television cewa wasu yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kai hari a garuruwan uku da asubahin ranar Alhamis suna harbe harbe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel