An kama dagajin ƙauye da ke haiƙe wa ƴarsa mai shekara 15

An kama dagajin ƙauye da ke haiƙe wa ƴarsa mai shekara 15

Dagajin ƙauyen Oose Agbedu Ajibawo a Owode-Yewa, a ƙaramar hukumar Yewa ta Kudu na jihar Ogun, a ranar Alhamis ya suma an garzaya da shi asibiti bayan an gabatar masa da hujjar cewa yana yi wa yarsa fyaɗe.

Dagajin ƙauyen da ƴan sanda suka kama saboda zargin yi wa yarsa mai shekaru 15 fyade, ya musanta zargin da ake masa.

Amma yayinda ɗaya daga cikin tsohuwar matarsa ta gaskata zargin da ƴarsa ta yi, ya yanke jiki ya faɗi sumamme kuma aka garzaya da shi asibiti inda ya farfaɗo a can.

Kakakin ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan ciki wata sanarwa da ya fitar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An kama basaraken da ya yi wa yar cikinsa fyade a Ogun
An kama basaraken da ya yi wa yar cikinsa fyade a Ogun
Asali: Twitter

Ya yi bayanin cewa yarinyar ta yi ƙorafin cewa mahaifinta ya kwashe shekaru hudu yana lalata da ita tun tana ƴar shekaru 11.

Kakakin ƴan sandan ya ce abin ya faru da ita ta koka cewa tana samun matsala da mafitsarar ta sakamakon abinda mahaifinta ya aikata.

DUBA WANNAN: Zulum ya naɗa sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

Ya ce, "wacce abin ya faru da ita ta shaida wa ƴan sanda cewa mahaifiyarta ta rasu lokacin tana da shekaru biyu kuma mahaifinta bai bari ta san ƴan uwan mahaifiyarta ba.

"Hakan yasa ba ta da zaɓi sai cigaba da zama tare da shi duk da cewa ya kan ci zarafin ta lokaci zuwa lokaci."

Kakakin ƴan sandan ya ce a lokacin hada wannan rahoton, DPO na Owode-Egbado, SP Olabisi Elebite da wasu ƴan sanda sun tafi gidan wanda ake zargin da wasu jami'ai sun kuma tiso ƙeyarsa.

A cewar Kakakin ƴan sandan, Rasheed, da farko ya musanta zargin da ake masa amma da ɗaya daga cikin tsohuwar matarsa da gaskata ƙorafin yarsa, wanda ake zargin ya faɗi sumamme.

Oyeyemi ya ƙara da cewa, "Tsohuwar matarsa ta sanar da ƴan sanda cewa ta taɓa kama shi yana lalata da ƴarsa hakan yasa aka raba auren su.

"An kai wacce abin ya faru da ita zuwa gidan marayu na Stella Obasanjo domin samun mafaka."

Kakakin ƴan sandan ya ce Kwamishinan yan sanda Edward Ajogun ya bayar da umurnin mika wanda ake zargin ga sashin masu yaƙi da safarar yara da cin zarafin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel