Bayelsa: Dakarun soji sun kutsa sansanin tsageru, sun kashe 6

Bayelsa: Dakarun soji sun kutsa sansanin tsageru, sun kashe 6

Hedkwatar tsaro ta kasa ta ce dakarun sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Delta Safe, a ranar Talata, a jihar Bayelsa, sun kai samame wani sansanin 'yan fashin teku inda suka kashe 'yan ta'adda shida.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar sojin Najeriya, John Enenche, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.

Kamar yadda kakakin rundunar ya sanar, dakarun sun yi aiki ne a kan bayanan sirri tare da kiyaye kaiwa da kawowar wanda suke zargin, wanda shine shugaban 'yan fashin tekun wanda ya shiga garin daga Fatakwal.

Daga bisani rundunar ta kai samame sansanin Tukugbene-Ayama da ke karamar hukumar Ijaw, inda aka kama wadanda ake zargin tare da sauran mambobin kungiyar.

Janar Enenche ya bayyana cewa, bayan isa sansanin wadanda ake zargin, rundunar ta budewa 'yan fashin dajin wuta wadanda ke jiragen ruwa biyar kuma suna kusanto wurin.

Ya kara da bayyana cewa, an samu bindigogi kirar AK47 guda uku tare da harsasai, janareto guda biyu kirar Yamaha duk sojin sun kwace.

Dakarun soji sun kashe kutsa sansanin tsageru, sun kashe 6
Dakarun soji sun kashe kutsa sansanin tsageru, sun kashe 6. Hoto daga Channels TV
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An sako masu zanga-zangar juyin juya hali da aka kama a Abuja

Hedkwatar tsaron ta jinjinawa zakakuran dakarun a kan kokarinsu tare da shawartar su da su dage wajen kawo karshen al'amuran ta'addanci da tsageranci na teku da ya addabi yankin Neja Delta.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Borno ta kama wasu 'yan ta'adda 45 a sassa daban-daban na jihar a kan laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane.

Daya daga cikin 'yan ta'addan mai suna Goni Mallum, ya amsa laifinsa na samarwa 'yan ta'addan kayayyakin bukatu amma ya ce yunwa da fatara ce ta sa shi yin hakan.

Mallum ya ce 'yan ta'addan sun kama shi a kan hanyarsa ta zuwa gona amma sun yanke shawarar kyale shi idan ya amince zai dinga yi musu aike-aike a kyauta, lamarin da ya kasa musantawa.

Manoma masu tarin yawa a jihar Borno suna fuskantar barazana irin wannan ko ta kisa yayin da aka kai musu hari a gonakinsu, yayin da wasu ke rayuwarsu a sansanin 'yan gudun hijira.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel