Wani mutum ya kai hari fadar White House, ya tilastawa Trump guduwa daga dakin taro

Wani mutum ya kai hari fadar White House, ya tilastawa Trump guduwa daga dakin taro

Jami'an tsaron asirin dake tsaron fadar shugaban kasan Amurka, White House, sun dauke shugaban kasar , Donnald Trump, daga dakin taro sakamakon harbe-harben da aka fara ji a wajen harabar fadar.

Yan mintuna da fara hira da manema labarai ranar Litnin, dogaran Trump suka garzaya wajensa yayinda yake jawabi kan mumbari kuma sukayi gaba da shi.

Dogarin ya ce masa, "Yallabai biyo ni mu tafi."

Ba tare da bata lokaci ba, Trump da mukarrabansa suka wuce kuma aka garkame kofar dakin taron cike da yan jarida.

A wajen fadar, an ga jami'an tsaro suna guje-guje suna boyewa bayan bishiyoyi. A cewar Fox News, wadanda kamarorinsu ke waje, an ji harbe-harbe har sau biyu.

KU KARANTA: 'Ta'addanci ne': Cacar baki ta kaure a kan hukuncin kashe matashi saboda batanci ga Annabi

Wani mutum ya kai hari fadar White House, ya tilastawa Trump guduwa daga dakin taro
fadar White House
Asali: Facebook

Daga baya Trump ya dawo dakin taron inda yayi bayanin cewa an bindige maharin kuma an garzaya da shi asibiti.

Trump ya ce lokacin da jami'an tsaro suka fita da shi, ofishin Oval suka kaishi .

"Harbi aka ji a wajen fadar White House. Amma komai yayi daidadi yanzu... Amma anyi harbe-harbe kuma an garzaya da wani asibtii. Ban san halin da yake ciki ba." Trump yace.

Daga bayan hukumar tsaron fadar White House, ta saki jawabin cewa "daidai misalin karfe 5:53 na yamma wani mahari ya kaiwa jami'in tsaro dake gadin fadar hari kuma ya ciro wani abu daga aljihunsa.

"Ganin kaman cewa ya ciro makamai, hakan ya sa jami'in tsaro ya bindigeshi." Jawabin hukumar yace.

An garzaya da mutumin da jami'in tsaron asibiti kuma za'a binciki lamarin, hukumar ta kara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel