An kashe mutum 20 a sabon harin da aka kai a Kaduna

An kashe mutum 20 a sabon harin da aka kai a Kaduna

A kalla mutum 20 ne suka riga mu gidan gaskiuya kuma wasu da dama suka jikatta sakamakon sabbin hare haren da aka kai a wasu garuruwa uku a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce ana zargin yan daba ne suka kai harin da ya faru a ranar Alhamis kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Garruruwan da aka kai harin sun hada da Kurmin Masara, Apyia Shyim, and Takmawai .

Wannan sabbin harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan an tura jami'an tsaro zuwa wasu garruruwan da ake ganin sun cikin hatsari ko kuma rikici na iya barkewa.

An kashe mutum 20 a sabon harin da aka kai a Kaduna
An kashe mutum 20 a sabon harin da aka kai a Kaduna. Hoto daga Channels TV
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Soja da ta yi ciki bayan ƴan bindiga sun mata fyade ta daukaka kara kan korarta daga aiki

Sufeta Janar na Yan sanda, Mohammed Adamu ya umurci kwamishinan yan sandan jihar ya tura jamiansa domin kare rayuka da dukiyoyin mutanen garuruwan da abin ya shafa.

Rundunar yan sanda ba ta tabbatar da harin ba amma shugaban karamar hukumar Zangon Kataf, Elias Manza ya shaidawa Channels Television cewa wasu yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kai hari a garuruwan uku da asubahin ranar Alhamis suna harbe harbe.

Ya yi bayanin cewa an kashe mutum bakwai a Takmawai yayin da an kashe wasu 13 a Kurmin Masara a wani abinda ya yi kama da harin da aka tsara.

Har ila yau, Manza ya ce maharan sun kone gidaje da dama yayin da mazauna garin da dama sun yi hijira zuwa kauyukan da ke makwabtaka da su domin tsoron kada a sake kawo wani harin.

Idan za a iya tunawa, gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar ta baci na awa 24 a kananan hukumomin Zangon Kataf da Kauru a ranar 11 ga watan Yunin 2020.

Gwamnan jihar, Nasir El Rufai ya danganta harin da ake kai wa a jihar musamman kudancin jihar da yan bindiga.

Kwanaki kadan a suka shude gwamnan ya gana da masu sarautun gargajiya inda ya nemi taimakon su domin kawo karshen kashe kashen.

Gwamnan ya jadadda cewa ya zama dole a hada hannu domin kawo karshen rikicin da ya ki ci ya ki cinye wa a wasu sassan jihar.

Ya kuma kallulancin masu sarautun gargajiyan su tona asirin bata gari da ke cikinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel