Yanzu-yanzu: Bayan shekara 1, an rantsar da zababbun yan majalisar dokokin Edo 12 mabiya Oshiomole (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Bayan shekara 1, an rantsar da zababbun yan majalisar dokokin Edo 12 mabiya Oshiomole (Hotuna)

Bayan shekara daya da kauracewa majalisar dokokin jihar Edo, an rantsar da zababbun yan majalisan jam’iyyar All Progressives Congress APC 12 yanzu haka a birnin Benin.

Zaku tuna cewa bayan kammala zaben yan majalisar dokokin jihar Edo a Mayun 2019, an yi rikici kan wadanda za’a zaba shugabannin majalisar musamman Kakaki.

Ana cikin rikicin wasu yan majalisa 9 da ake kyautata zaton na da goyon bayan gwamnan suka shiga zauren majalisar cikin dare suka gudanar da zaben kuma suka zabi Kakaki Frank Okiye.

Tun daga lokacin sauran yan majalisun 12 suka ce ba zasu sake zuwa zauren majalisar ba kuma ba za’a rantsar da su ba.

Yanzu-yanzu: Bayan shekara 1, an rantsar da zababbun yan majalisar dokokin Edo 12 mabiya Oshiomole (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Bayan shekara 1, an rantsar da zababbun yan majalisar dokokin Edo 12 mabiya Oshiomole (Hotuna)
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun farke rufin majalisar Edo, sun sace sandar iko

Makon da ya gabata yan majalisa 5 cikin 9 dake zama suka sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC kuma suka alanta goyon bayansu da ga dan takaran kujeran gwamnan APC, Fasto Osaze Ize-Iyamu.

Daga cikin wadanda suka sauya sheka shine mataimakin kakain majalisar Yekini Idiaye.

Sauran sune Emmanuel Agbaje mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta biyu, Nosayaba Okunbor mai wakiltar mazabar Orhionmwon ta gabas, Dumez Ugiagbe mai wakiltar mazabar Ovia ta arewa maso gabas.

Da safen nan 'Yan sanda sun mamaye farfajiyar majalisar jihar Edo, sa'o'i kadan bayan tsige mataimakin kakakin majalisar, Yekini Idiaye, wanda 'yan majalisar jihar suka yi a ranar Laraba.

Yanzu haka zababbun yan majalisun 12 da suka ki shiga majalisar tun 2019 sun dawo a rantsar su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel