Rikici ya raba kawunan 'yan jam'iyyar PDP a Niger

Rikici ya raba kawunan 'yan jam'iyyar PDP a Niger

Rikici ya kuna kai a jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, reshen jihar Niger kwanaki kadan kafin babban taron ta har ta kai ga jam'iyyar ta rabu kashi biyu.

An ruwaito cewa matakin da sakatariyar jam'iyyar na kasa ta dauka na sake fara sayar da tikitin shiga takara bayan ta rufe a baya ne ya janyo rabuwar kawuna a jam'iyyar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Bangare guda a jamiyyar na goyon bayan sake bayar da damar sayar da fom din takarar yayin da dayan bangaren kuma na ganin wannan matakin da aka dauka ya saba wa kundin tsarin jam'iyyar.

Jam'iyyar PDP a Niger ta rabu gida biyu
Jam'iyyar PDP a Niger ta rabu gida biyu
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An yi sulhu tsakanin Bafarawa da Wamakko

Tsohon mataimakin gwamnan jihar, Dr Zagbayi Nuhu, wanda ke magana da yawun 'Yan kishin PDP a jihar ya shaidawa manema labarai a Minna a ranar Laraba cewa saka fara sayar da fom bayan wa'adin da aka bayar na sayar da fom din ya wuce watanni hudu da suka shude ba dai dai bane.

Ya bukaci sakatariyar jam'iyyar na kasa ta duba lamarin kafin abubuwa su tabarbare.

Ya kuma shaida wa sakatariyar jamiyyar na kasa kada ta sake ta dage babban taron jam'iyyar da aka shirya yi domin jihar ta shirya zaben shugabannin ta a lokacin.

A martanin da ya mayar cikin gaggawa, Shugaban kwamitin rikon kwarya na jihar, Garba Ciza ya ce sakatariyar na kasa ne ta dauki matakin sake bude sayar da fom din kuma abin ya shafi jihohi da dama a kasar.

"Sakatariyar jam'iyyar mu ta kasa ne ta amince a sake bude sayar da fom din domin bawa wasu mutane da ke shaawar shiga takarar dama musamman wadanda da farko aka tantance su," a cewar Ciza.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel