Da duminsa: Jami'an tsaro sun zagaye majalisar jihar Edo

Da duminsa: Jami'an tsaro sun zagaye majalisar jihar Edo

'Yan sanda sun mamaye farfajiyar majalisar jihar Edo, sa'o'i kadan bayan tsige mataimakin kakakin majalisar, Yekini Idiaye, wanda 'yan majalisar jihar suka yi a ranar Laraba yayin zaman majalisar a Benin City.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta 1 da wasu 'yan majalisa hudu a ranar Litinin sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar kujerar gwamna karkashin jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Wadanda suka bi ayarin Idiaye sune Emmanuel Agbaje mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta biyu, Nosayaba Okunbor mai wakiltar mazabar Orhionmwon ta gabas, Dumez Ugiagbe mai wakiltar mazabar Ovia ta arewa maso gabas.

Duk sun bayanna goyon bayansu ga Fasto Ize-Iyamu a gidan sa da ke Benin.

Amma kuma Roland Asoro, mai wakiltar mazabar Orhionmwon II an nada shi a matsayin mataimakin kakakin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel