Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata

Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata

Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta kama wasu 'yan ta'adda 45 a sassa daban-daban na jihar a kan laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane.

Daya daga cikin 'yan ta'addan mai suna Goni Mallum, ya amsa laifinsa na samarwa 'yan ta'addan kayayyakin bukatu amma ya ce yunwa da fatara ce ta sa shi yin hakan.

Mallum ya ce 'yan ta'addan sun kama shi a kan hanyarsa ta zuwa gona amma sun yanke shawarar kyale shi idan ya amince zai dinga yi musu aike-aike a kyauta, lamarin da ya kasa musantawa.

Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata
Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

Manoma masu tarin yawa a jihar Borno suna fuskantar barazana irin wannan ko ta kisa yayin da aka kai musu hari a gonakinsu, yayin da wasu ke rayuwarsu a sansanin 'yan gudun hijira.

Mallum ya yi wa jami'an tsaron da suka damke shi bayanin yadda yake ayyukansa. Manomin ya ce an kama shi ne a yayin da yaje siyowa mayakan ta'addancin magunguna.

Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata
Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

"Sun rubuta min dukkan abinda suke bukata sun bani duk da ban san me suka rubuta ba. Na je shago siya Ashe abubuwa ne masu tarin hatsari," Mallum ya sanar da manema labarai a tattaunawar da suka yi.

KU KARANTA: Rashin takunkumi: Hotunan jami'an tsaro na lalata da budurwar da suka kama a cikin mota

Ya kara da cewa, mai shagon ne ya kai wa JTF labari kuma kungiyar 'yan kasuwan suka kama shi. Na san ban kyauta ba, amma yunwa ce ta sa ni yin hakan. "Ina siyar da hatsi a Muna Garage amma na rasa jari na kuna banda aikin yi."

Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata
Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno, DSP Edet Okon, ya ce an kama Mallum ne sakamakon bibiyarsa da aka yi kuma za a mika shi kotu sakamakon laifin ta'addancin da ya aikata tare da taimakawa wurin aikata laifi.

"Wanda ake zargin ya amsa laifinsa na samar da kayayyakin bukata ga mayakan ta'addancin," yace.

Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata
Boko Haram: 'Yan sanda sun damke Mallum, mai samarwa 'yan ta'adda kayan bukata. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

Sauran wadanda aka kama da laifuka sun hada da 'yan fashi da makami, satar dabbobi, damfara, cin amana, garkuwa da mutane da sata.

DSP Edet ya ce dukkansu za a mika su gaban kuliya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel