Fani-Kayode: Sarkin Shinkafi ya amince da murabus din masu sarauta 5, ya maye gurbinsu
Sarkin Shinkafi, Muhammad Makwashe Isa, ya amince da murabus na mambobin majalisarsar biyar wadanda suka ajiye rawani don rashin amincewa da sarautar da aka bai wa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode.
Idan za mu tuna, a makonni kadan da suka gabata ne Sarkin Gabas ya bai wa lauya dan asalin jihar Legas mai shekaru 59 sarautar Sadaukin Shinkafi, abin da ya janyo cece-kuce inda wasu suka danganta hakan da siyasa.
Bayan kwanaki kadan, Bilyaminu Yusuf, Sardaunan Shinkafi; Umar Ajiya, Dan Majen Shinkafi; Hadiza Abdulaziz Yari, Iyar Shinkafi; Dr Tijjani Salihu Shinkafi, Uban marayun Shinkafi; da Dr Suleiman Shuaibu, Sarkin Shanun Shinkafi suna mika wasikar murabus dinsu a kan nadin sarautar.
A wata takarda da sarkin ya fitar a ranar Laraba ta hannun Ibrahim Muhammad, Sarkin Sudan Shinkafi, ya ce ya samu wasikunsu kuma ya sanar da wadanda za su maye gurbinsu.
Takardar ta ce: "Mai martaba ya amince da nadin Aliyu Jibril Guraguri a matsayin Sardaunan Shinkafi, Umar Abdullahi a matsayin Dan Majen Shinkafi, Bello Hassan Shinkafi a matsayin Uban Marayun Shinkafi da Dr. Usman Muhammad a matsayin Sarkin Shanun Shinkafi.
KU KARANTA: Rashin takunkumi: Hotunan jami'an tsaro na lalata da budurwar da suka kama a cikin mota
Sarkin ya amince da nadin wasu daga cikin 'yan gidan sarautar Shinkafi da sarauta Kamar haka: Sulaiman Mani a matsayin sallamar Shinkafi, Rabiu Dahiru a matsayin Barayan Shinkafi, Bello Umar a matsayin Bunun Shinkafi, Dr. Ibrahim Jibril Hanu a matsayin Wakilin Lafiyar Shinkafi da Dr. Ibrahim Hassan a matsayin Tudun Shinkafi.
Sannan Abba Atiku a matsayin Gwarzon Shinkafi, Ibrahim Bama a matsayin Gabdon Shinkafi, Fatima Sa'id Aran a matsayin sarauniyar Shinkafi, Abdullahi Sani a matsayin Dan Isan Shinkafi, Dr. Aminu Alhazai a matsayin Wakilin Maganin Shinkafi da Abdullahi Muhammad Maitaurari a matsayin Jakadan Shinkafi.
Sauran suna hada da Hindatu Muhammad Maitaurari a matsayin Kilishin Shinkafi, Lawalo Moyo a matsayin Lihdin Shinkafi, Kabiru Ibrahim a matsayin Mu'allakin Shinkafi, Ashiru Ibrahim Dangishiri a matsayin Dan Amanar Shinkafi da Ashiru Umaru Nagwanadu a matsayin Sarakin Shinkafi.
Kakakin masarautar ya tabbatar da cewa za a sanar da ranar shagalin bikin nadin sarautar babu dadewa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng