Da duminsa: Shugaba Buhari ya nada AbdulMumini Jibrin wani babban mukami

Da duminsa: Shugaba Buhari ya nada AbdulMumini Jibrin wani babban mukami

- Tsohon dan majalisar wakilai, AbdulMumini Jibrin ya samu mukami daga shugaban kasa

- Jawabi daga hadimin gwamnan Kano ya nuna gwamna Ganduje yana tayashi murna

- Jibrin ya samu matsala da jam'iyyar APC a jihar Kano kuma hakan ya ja masa rasa kujeransa a majalisa

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada tsohon dan majalisa, AbdulMumini Jibrin a matsayin sabon Diraktan hukumar gidajen tarayya (sashen cigaban kasuwanci, da samar da gidaje ga jama'a)

Hakan ya bayyana cewa a jawabin hadimin gwamna Abdullahi Ganduje kan labarai, Salihu Tanko Yakassai, ranar Laraba 5 ga Agusta, 2020.

Yakassai ya ce gwamnan ya taya Jibrin murna kan sabon matsayinsa kuma ya godewa shugaba Buhari bisa wannan amincewa da yayi da Jibrin.

Da duminsa: Shugaba Buhari ya nada AbdulMumini Jibrin wani babban mukami
Da duminsa: Shugaba Buhari ya nada AbdulMumini Jibrin wani babban mukami
Source: Twitter

KU KARANTA: Idan aka hana kabilar Igbo shugabancin kasa a 2023, zamu hada kai da Nnamdi Kanu - Tsohon shugaban PDP

Haka kuma a jihar Kano, Kungiyar yan kasuwan man fetur masu zaman kansu IMAN, shiyar jihar , ta umurci mambobinta su fara sayar da man fetur a farashin N150 ga lita.

Daily Nigerian ta ce a jawabin da ya saki, shugaban kungiyar na jihar Kano, Bashir Dan-Mallam, ya ce umurnin ya biyo bayan sabon farashin sauyin farashin mai da kamfanin PPMC, mai hakkin sanya farashin mai.

A cewarsa, wannan mataki da suka zamu ya yi daidai da jawabin gwamnati cewa za ta rika canza farashin mai wata-wata dangane da yadda farashin ya canza a kasuwar duniya.

Dan Mallam ya hakaito jawabin PPMC inda ta ce an kara farashin kayan mai zuwa N138.62 ga lita a depot.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel