Idan aka hana kabilar Igbo shugabancin kasa a 2023, zamu hada kai da Nnamdi Kanu - Tsohon shugaban PDP

Idan aka hana kabilar Igbo shugabancin kasa a 2023, zamu hada kai da Nnamdi Kanu - Tsohon shugaban PDP

Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Okwesilieze Nwodo, ya ce idan ba'a baiwa kabilar Igbo shugabancin kasa a 2023 ba, masu arzikin kudu maso yamma zasu hada kai da shugaban kungiyar yakin neman Biyafara IPOB, Nnamdi Kanu wajen ballewa daga Najeriya.

Nnamdi Kanu ya kasance kan gaba wajen yakin neman yancin yankin kabilar Igbo saboda yadda aka mayar da yan yankin saniyar ware.

Ya tsere daga Najeriya bayan samun beli daga kotu.

A hirar Okwesilieze Nwodo da jaridar Vanguard, ya jinjinawa Tanko Yakassai, bisa kiran da yayi a baiwa Igbo shugabancin kasa a 2023.

Ya ce shekaru 50 kenan ana cin zarafin Igbo, kuma ya shawarci dukkan masu son rana goben yaransu yayi kyau su zabi Igbo a 2023.

Idan aka hana kabilar Igbo shugabancin kasa a 2023, zamu hada kai da Nnamdi Kanu - Tsohon shugaban PDP
Idan aka hana kabilar Igbo shugabancin kasa a 2023, zamu hada kai da Nnamdi Kanu - Tsohon shugaban PDP
Asali: UGC

A jamhurriya ta farko, Tafawa Balewa ya jagoranci kasar, a jamhurriya ta biyu, Shehu Shagari ya jagoranci kasar, kuma daga baya mu da muke PDP, munyi yunkurin mayar da shugabancin kasa wajen Igbo, saboda ko a gidan Soja duk yan Arewa ne, baicin Aguiyi Ironsi da yayi mulki cikin dan kankanin lokaci," Yace

"Shekaru 50 yanzu, ana cin zarafinmu don muna neman yanci. Yaushe wannan wariyar zai zo karshe?

"Dan kabilar Igbo ne mutum daya tilo da ba zai nuna wariya ga kowani sashen Najeriya ba saboda mu ne mahadin dake rike kasar nan."

"Mu kadai ne kabilar da za ka samu a lungu da sakon kasar nan muna kasuwanci kuma muna inganta wajen tamkar namu ne."

"Na yarda da Nnamdi Kanu a dukkan abubuwan da yake fada kan wariyar da ake nunawa Igbo...Idan Najeriya na kokarin bayyanawa attajiran Igbo cewa su bare ne kuma ba zasu taba shugaban kasa ba, kusan dukkansu zasu hada kai da Kanu wajen yakin neman Biafra."

"Domin adalci da daidato, Najeriya ta baiwa kudu maso gabas shugabancin kasa a 2023, idan ba haka ba, zamu hada kai da shi wajen yakin neman Biyafara."

A makon da ya gabata, kungiyar matasan Ohanaeze ta bayyana cewa adalci da nuna daidaiton da shugaba Muhammadu Buhari zai iya yi kadai shine ya mika ragamar mulki hannun dan kabilar Igbo a 2023,

Yan kungiyar sun jaddada cewa yanzu ne karon yankin kudu maso gabas na gadan kujerar shugaban kasa.

A cewarsa, don nuna daidaito, tabbatar da zaman lafiya, da nuna adalci, ya kamata yan Najeriya, musamman yan Arewa su goyi bayan yan kabilar Igbo.

"Buhari ya mika mulki ga dan takaran Igbo a 2023. Ya bayyana karara yanzu ne karon yankin Kudu maso gabas a 2023." Dozie yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel