Yanzu-yanzu: Yan ta'addan Al-Qa'ida sun fara shiga jihohin Arewa maso yamma - Amurka ta ankarar da Buhari

Yanzu-yanzu: Yan ta'addan Al-Qa'ida sun fara shiga jihohin Arewa maso yamma - Amurka ta ankarar da Buhari

Gwamnatin kasar Amurka ya bayyanawa duniya cewa mambobin kungiyar yan ta'addan Al-Qa'ida sun fara ratsawa jihohin Arewa maso yammacin Najeriya.

Kwamandan Sojin Amurka na harkoki na musamman a nahiyar Afrika, Dagvin Anderson, wanda ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai ya ce kungiyar na shiga wurare daban-daban a yammacin Afrika.

A jawabin da TheCable ta samu daga ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Anderson ya ce Amurka za ta cigaba da hada kai da Najeriya wajen raba bayanan binciken sirri.

Jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sune: Kaduna, Kano, Katsina, Jigawa, Zamfara, Kebbi, da Sokoto.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fara feshin makarantu 19,000 da za'a zana jarabawar WAEC

Yanzu-yanzu: Yan ta'addan Al-Qa'ida sun fara shiga jihohin Arewa maso yamma - Amurka ta ankarar da Buhari
Yanzu-yanzu: Yan ta'addan Al-Qa'ida sun fara shiga jihohin Arewa maso yamma - Amurka ta ankarar da Buhari
Asali: UGC

"Muna hada kai da Najeriya kuma zamu cigaba da hadawa wajen raba bayanan sirri da wajen fahimtar abubuwan da wadannan yan ta'addan ke yi."

"Kuma hakan ya taimaka musu wajen ayyukansu a jihar Borno da kuma Arewa maso yammacin Najeriya da muka ga yan Al-Qa'ida sun fara shiga."

"Amma matsayinmu na al'ummar kasashen duniya, mu kan yi tunanin mun kawar da su ne kuma suna gab da wargajewa."

"Ina tunanin bayan shekaru 20 mun gano cewa suna da taurin kai, duk da kanana ne, suna amfani da kafafen sada zumunta wajen daukan sabbin mambobi kuma suna samu." Yace

Anderson ya ce abinda zai sa kokarin kasashen duniya ya haifi da mai ido shine idan gwamnatin Najeriya da kanta tayi hobbasa wajen gudanar da yaki.

"Idan aka zo lamarin Najeriya kuwa, Najeriya na da muhimmanci ga yankin Afrika ta yamma."

"Saboda haka babu kasar da za ta magancewa Najerita matsalarta. Zamu iya taimakawa, Birtaniya da sauran kasashe zasu iya taimakawa, amma wajibi ne Najeriya ta tashi tsaye domin mu san da gaske take." Yace

Ana fuskantar hare-hare a jihohin Arewa maso yamma musamman Katsina, Sokoto da Zamfara.

A baya Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa Rahotanni na yawo cewa wasu dinbin ‘tan ta’addan kungiyar Boko Haram na bangaren Abubakar Shekau, sun fitar da sabon bidiyo na musamman.

‘Yan ta’addan da su ka yi wa Abubakar Shekau mubaya'a sun ce sun dauki wannan bidiyo ne a jihar Neja da ke a yankin Arewa maso tsakiyar kasar.

Malam Audu Bulama Bukarti, wani masanin harkar tsaro ya bayyana wannan a shafinsa na Twitter dazu. A wannan bidiyo an ga mutane kimanin dari su na gabatar da sallar idi a kungurmin daji.

Daga baya wasu sojoji uku su ka yi jawabin barka da sallah. Wadannan mayaka sun yi magana ne da harshen Hausa, Ingilishi da kuma Fulfulde.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel