Tsaro: Buhari ya gana da Masari a Abuja
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba 5 ga watan Augustan shekarar 22.
Masari ya ce ba za a bari kallubalen tsaro da ake fama da ita a jihohin Arewa maso Yamma da Arewa maso tsakiya ya tabarbare kamar matsayin da Boko Haram ya kai a Arewa maso Gabas.

Asali: Twitter
Masari ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke amsa tambayar manema labarai a gidan gwamnatin bayan kammala taro da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Yaki da COVID-19: Ganduje ya zama gwarzo a tsakanin gwamonin Najeriya
Ya ce a halin yanzu ana daukan dukkan matakan da suka dace domin kawo karshen hare haren yan bindiga da wasu laifukan a yankin na Arewa maso Yammacin kasar.
Gwamnan ya ce za a samu amfanin gona mai kyau a bana duk da cewa yan bindiga da wasu bata gari sun adabi manoma a kimanin kananan hukumomi tara a jihar ta Katsina.
Ku dakaci cikaken rahoton...
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng