Da duminsa: Majalisar jihar Edo ta yi sabon mataimakin kakaki

Da duminsa: Majalisar jihar Edo ta yi sabon mataimakin kakaki

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Orhionmwon ta biyu a majalisar jihar Edo, Roland Asoro, ya zama mataimakin kakakin majalisar jihar Edo ta Najeriya.

An nadasa ne bayan tsige Yekini Idiaye a matsayin mataimakin kakakin majalisar.

Idiaye, dan majalisa mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta daya, an tsigesa ne a ranar Laraba a yayin zaman zauren majalisar a Benin City, babban birnin jihae Edo.

An tsigesa bayan kwanaki uku da ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC, Fasto Osagie Iyamu.

Legit.ng ta ruwaito cewa, an tsige mataimakin kakakin majalisar jihar Edo, Yekini Idiaye a yau ranar Laraba. An tsigesa ne a ranar Laraba yayin zaman zauren majalisar a Benin City.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta daya da wasu 'yan majalisar hudu sun tabbatar da goyon bayansu ga dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Wadanda suka bi ayarin Idiaye sune Emmanuel Agbaje mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta biyu, Nosayaba Okunbor, mai wakiltar Orhiomwon ta gabas, Dumez Ugiagbe, mai wakilatar mazabar Ovia ta arewa maso gabas.

Dukkansu sun tabbatar da cewa suna goyon bayan Fasto Ize-Iyamu bayan ziyarar goyon baya da suka kai gareshi.

KU KARANTA: Dandanon budurcinta nayi - Dan achaba da ya yi lalata da diyar cikinsa

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel