2023: Tanko Yakassai, Mbazulike Amechi sun goyi bayan shugabancin kabilar Ibo

2023: Tanko Yakassai, Mbazulike Amechi sun goyi bayan shugabancin kabilar Ibo

Daya daga cikin manyan dattawa a Najeriya, Alhaji Tanko Yakasai, ya ce babu yankin da kamata ya samar da shugaban kasa a 2023 face Kudu maso Gabashin Najeriya.

Dattijon dan asalin jihar Kano ya ce ya dace kabilar Ibo ta samar da shugaban kasar nan a yayin da tarihi ya tabbatar da cewa ba ta samun damar hakan ba.

Alhaji Yakasai ya yi furucin hakan yayin hira a wani shiri na gidan Talabijin Na AriseNews da aka yi da shi ranar Talata a jihar Legas, inda ya ce dole shugabanci sai an tashi an nema.

Da wannan ne yake shawartar manyan ‘yan siyasa na kabilar Ibo, da su fita neman goyon bayan ‘yan Najeriya a sauran yankunan kasar domin cimma burinsu na samar da

“Ina matukar jin tausayin ‘yan kabilar a yayin da har kawo yanzu a tarihin Najeriya basu taba samar da shugaban kasa ba.”

“Yankin Kudu maso Yamma, Kudu maso Kudu da kuma na Arewa duk sun taba dandana kujerar mulki a yayin da an bar Kudu maso Gabas a baya.”

Alhaji Tanko Yakasai
Alhaji Tanko Yakasai
Asali: UGC

“Sai dai koda yake, babu mai iya ba wa mutum mulki yana zaune, dole sai ya tashi ya fafata wajen nemansa.”

“Saboda haka ina fatan yankin Kudu maso Gabas zai fita neman goyon bayan sauran yankunan kasar.”

“Mu a Arewa, bamu da wata matsala da ‘yan kabilar Ibo. Akwai inyamurai a kowane kauye na Arewa inda suke gudanar da harkokin kasuwanci.”

“Yarbawa sun fi mu wuyar sha’ani ta fuskar shawo kansu da gamsarwa, saboda haka wurinsu ya kamata Inyamurai su je neman goyon baya.”

Da yake martini dangane da ra’ayin Alhaji Yakasai, wani dattijon kasar kuma fitaccen jagoran kabilar Ibo, Cif Mbazulike Amechi, ya amince a kan hakan.

KARANTA KUMA: Fiye da jami'o'i 32 sun ba da gudunmuwar yaki da cutar korona a Najeriya - NUC

Mbazulike Amechi, shi ne tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya tun a jamhuriya ta farko.

Ya ce samar da shugaban kasa daga tsatson kabilar Ibo ba lamari bane da za a yi ta babatu ko muhawara a kai, "babbar bukata ita ce tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaba mai dorewa a kasar.

“Ni da Tanko Yakasai mun kasance aminan juna tun kafin Najeriya ta samu ‘yancin kai, kuma har yanzu akwai kyakkyawar alaka a tsakaninmu.

“A wasu lokuta ‘yan kalilan mu kan samu sabani a fannin ra’ayin siyasa, amma hakan ba ya tasiri a kan dangartakar da ke tsakaninmu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel